Daga Hussaini Garba Mohammed
kasar Indiya na da wuraren shakatawa na lambuna masu ban sha’awa. Wadannan wurare masu ban sha’awa ne suke bunkasa harkokin fina-finai da al’amuran yawon shakatawa.
Mafi yawanmu da ke sha’awar kallon fina-finan Indiya, mun sha ganin yadda jaruman fim ke taka rawa a cikin wadannan kawatattun lambuna. A lokuta da dama mukan ga cewa mahaifin jarumi ko jarumar fim kan kasance hamshakin mai arziki a cikin katon gidaje, wadanda aka kawata su da shuke-shuken furanni a cikin lambuna.
A wannan shekarar da ta gabata, na samu damar kai ziyara a wurare da dama a fadin Indiya, har zuwa inda suke shirya fina-finai, wadanda na taba gani a shekaru da dama da suka wuce. daya daga cikin wadannan birane shi ne birnin Chandigarh.
Wannan birni na Chandigarh, shi ne birnin da aka fara tsarawa a kasar Indiya, kuma a shekarar 2010 an ruwaito cewa shi ne birni mafi tsafta a Indiya. Bayan an raba kasar Indiya gida biyu shekarar 1947, tsohuwar gundumar Punjab da ke karkashin Birtaniya, an raba gida biyu, inda aka samu Punjab ta Gabas, da Punjab ta Yamma, wadda ta fada cikin kasar Pakistan.
Yankin Punjab da ke Indiya, ya bukaci sauya babban birni, saboda Lahore ta fada cikin kasar Pakistan a lokacin da aka raba kasar. Sai aka samo sunan Chandigarh, wanda ma’anarsa na nufin “Farfajiyar Chandi.” Kuma asalin wannan suna an samo shi ne daga wani abin bautar addinin Hindu da ake kira Chandi Mandir da ke kusa da birnin. Wannan birni yana kusa da tsaunukan Sibalik da suka hadu da sassan tsaunukan Himalaya da ke Arewa Maso Gabashin Indiya.
Wannan birni yana da yanayin zafi kuma saukar ruwan sama ba shi da tabbas: Ana iya samu ko a rasa. A tsakiyar watannin Yuni da Satumba, Chandigarh na samu ruwan sama mai yawan gaske.
Birnin Chandigarh na da lambuna da wuraren shakatawa, don haka wasu ke yi wa birnin lakabi da ‘Birnin Kyau,’ ko ‘Birnin Zaman Lafiya,’ ‘Birnin Lambu,’ ko ‘Birnin Kimiyya’ da kuma ‘Birnin ’Yan Fansho’ ko ‘Birni Mai dimbin Dukiya,’ duk saboda mafi yawan al’ummar birnin, ko dai mutane ne da ke yi wa gwamanti aiki ko kuma sun yi murabus daga aikin gwamnati; tunda gwamnati ita ke da mafi yawan ’yan kwadago a kasar. Bisa wannan dalilin ake kiran birnin da lakabin ‘Birnin ’Yan Fansho.’
A shekarun baya, wani bincike da aka gudanar, an gano cewa wannan birni shi ne na tara a jerin birane 50 da harkokin fasahar sadarwar kwamfuta ke bunkasa, don haka kwararru a fannin fasahar sadarwa da kamfanoni ke neman bude ofisoshinsu a birnin. Sabanin sauran biranen da ke Indiya, wannan birni babu hayaniya a cikinsa. Birnin Chandigarh, birni ne da ake zaune lafiya kalau a cikinsa.
Fasalin zayyanar birnin, ta raba shi mai kusurwa hudu, ta yadda kowane rukuni na al’umma ke samun wurin zama, inda yawan mazaunan ke kamawa daga dubu biyar zuwa dubu 20. Kowace kusurwa na da babban kantin sayar da kayayyakin bukatun yau da kullum, ga makaranta da cibiyar kula da lafiya da wuraren shakatawa da wuraren ibada.
Idan mutum na neman wurin hutu da shakatawa da samun annashuwa a cikin tsirrai da furanni, to mutum zai so zuwa wannan birni, ya ziyarci lambunan cikinsa. Domin akwai dimbin furanni masu ban sha’awa, wadanda ke daukar hankali.
Akwai dimbin tsirran magani, don haka ba furanni masu ban sha’awa ne a birnin kawai ba suka sanya ya shahara a duniya. Na samu kai ziyara cikin mafi yawan wdannan lambuna, wadand suka hada da Lambun Mughal da na Taj Mahal da Red Fort da ke Delhi da Agra da ke Lambun Hindu da lambun Rajput.
Indiya na da tsohuwar al’adar tsara lambu sananniya a duniya. Mafi yawan wadannan lambuna na dauke da dabbobi da tsuntsaye, wadanda suka hada da agwagi da bareyi da aku da cakwaikwaiwa da tsuntsun sambar da dawisu, wadanda ke daukar hankalin baki, don haka suke tururuwa zuwa wuraren da aka kawata a wannan birnin. Mafi yawan wadannan lambuna suna da wuraren wasa, inda masu ziyara za su sauna su huta.
A cewar masu bincike da masanan kimiyya wadanda suka yi nazari kan tasirin furanni a kan rayuwa, inda suka yi nuni da cewa furannin kallo na da tasiri wajen sanya farin ciki. Za su iya sanya ka ka yi murmushi yayin da aka mika maka furen kallo. Suna kuma nuna karramawa da godiya, kamar yadda na fahimta.
Wannan al’amari yana aukuwa ga kowane rukuni na mutane a fadin duniya. Don haka na tuna da wani al’amari da ya auku da wani abokina mai tafiya Landan, wanda ya bar wasu kyaututtuka da za a bai wa abokinsa, wadanda suka hada da tukunyar furannin kallo kuma har a yanzu wanda aka bai wa wnanan kyauta yana alfahari da ita. Don a duk lokacin da ya bude kofar dakinsa, idan zai fita daga gida, ko zai shiga idan ya dawo daga aiki, sai ya yi sha’awar furannin da ya shuka a tukwanen.
Shekara hudu da suka wuce, na bai wa wata yarinya matashiya kyautar furanni, wadda bayan shekara hudun ta zama matata; mun kuma shafe watanni hudu muna tattaunawa ta waya. A lokacin da na hadu da ita, sai na dauki hankalinta da furanni, tamkar yadda Indiyawa ke yi. Wannan al’amari ya kara dankon soyayya a tsakaninmu. Kun ji yadda na mamaye zuciyarta, na bar ta Fulanin Adamawa cike da mamaki na tsawon rayuwa.
Wata safiya da gwamnatin Indiya ta bayar da bas don daukar mu zuwa lambunan shakatawa, mai yi mana jagora ya tambaye mu, ko mun taba jin labarin mutumin da ke dibar kayan juji, ya inganta su, ya sake alkinta su a cikin tsirrai da itatuwa? Sai muka ce “a’a,” shi kuwa ya ce: “Yau za mu kai ku ‘Lambun Dutse – Rock Garden. Na kasa wassafawa a tunani yadda wannan wurin shakatawa yake. Sai kawai jagoranmu ya ba mu labarin Nek Chand, wani ma’aikacin gwamnati a Indiya, wanda ya kafa wanan wurin shakatawa cikin sirri. Ya kuma shafe shekara 10 da rabi yana aiki, har sai da aka gano shi a gefen wani dutse, mai kewaye da furanni da tsirrai masu ban sha’awa da suka mamaye fadin kasa da ya kai eka 13.
An haifi Nek Chand a wani kauye da a halin yanzu yake cikin kasar Pakistan. Bayan samun ’yancin kasar daga hannun Birtaniya, sai ya koma kasar Indiya, inda ya ci gaba da aiki a matsayin jami’in kula da tituna a birnin Punjab. Da ma an rushe gine-ginen kauyuka fiye da 12, don a gina Chandigarh, wato birni mafi tsari a Indiya. Shi kuwa Nek Chand ya yi amfani da balgatattun gine-ginen da aka rushe, ya fitar da tsarin masarautar da ya wassafa a mafarkinsa, inda ya kafa Daular Sukrani. Chand ya shafe shekara 14 yana dibar ragowar rusassun gine-ginen a kan kekensa daga kasan tsaunukan Himalaya, yana shiga daji, don yin ginin da doka ba ta ba shi izini ba, har ya kammala a cikin wani daji da aka kafa tun a shekarar 1902. Duk da haka ya samu boye wannan gini nasa har tsawon shekara 18, kafin a gano shi cikin shekarar 1975.
A cikin wannan lambun tsauni na ‘Rock Garden’ na ga magudanun ruwa da gine-ginen laka kuma na cika da mamaki kan yadda magudanun ruwa suka tafi bisa tsari, tare da kawar furannin kallo. Akwai gadoji ’yan kanana.
A halin yanzu dai wannan shi ne birni na biyu da aka fi kai wa ziyara a birnin Indiya kuma fadinsa ya kai eka 40, bayan da gwamnatin Indiya ta bayar da tallafin inganta aikin.