✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaraba ga masu ciwon sukari a lokacin azumin watan Ramadan

Ina fata cikin yardar Allah, mai karatu a daidai lokacin da kake karanta wannan makala an samu kwanaki biyu ana azumin watan Ramadan na wannan…

Ina fata cikin yardar Allah, mai karatu a daidai lokacin da kake karanta wannan makala an samu kwanaki biyu ana azumin watan Ramadan na wannan shekarar ta 1436BH, daidai da 2015AD, wanda aka fara a jiya Alhamis. Azumin watan Ramadan na cikin shika-shikan Musulunci biyar, wanda ya wajaba a kan dukkan Musulmi da Musulma, wadanda suka balaga, masu cikakken hankali da lafiya. Wadanda rashin lafiyarsu za ta iya hana su yin azumin bisa ga shawarar likita, ko mace mai juna biyu ko mai shayarwa, ko tsoho ko tsuhuwa, (dukkan wadannan jinsin mutane akwai tanadin da shari`a ta yi masu a zaman ramuwa ko ciyarwa, a duk ranar da ba su iya yin azumin ba). Hatta kananan yara da ba su balaga ba, a kan karfafa masu gwiwa wajen ganin sun yi azumin na watan Ramadan, a zaman koya, zuwa lokacin da Allah zai sa su balaga.

Saboda muhimmancin watan azumi da Allah (SWT) ya bayyana farkon watan a zaman Rahama tsakiyarsa gafara, karshensa `yanta wuya. Sannan kuma shi kadai ne watan da Allah (SWT) ya tabbatar da ana rufe kofofin wuta ana bube na aljanna, kamar kuma yadda ake daure shedanu. Kazalika, wata ne da Allah yake nunnunka lada ga bayinsa wadanda suka yi ayyukan alheri, har ma ta kai yake cewa dukkan ayyukan alheri da mutum ya kan yi nasa ne amma azumi nasa ne, shi kadai zai saka wa wanda ya yi shi. Wata ne da Allah ya saukar da littafinsa mai tsarki (Alkur`ani). A cikin watan Allah yake saukar da daren Lailatul kadari, daren da ya fi wata dubu, daren da idan mutum ya dace aka amshi ibadarsa, to, shi ya yi gamo da katar a rayuwarsa.Domin ibadar wata dubu, daidai take da ta shekaru 83, har da watanni 4. Allah Ka rabautar da mu, amin summa amin.
A takaicen takaitawa, watan na Ramadan wata ne mai cike da falalar Ubangiji (SWT), kamar yadda su kansu Musulman duniya suke tabbatarwa a zamantakewarsu. Don za ka ga a cikinsa mutane suke kara dukufa da himmatuwa cikin yawaita ibada,kamar sallar farilla a cikin jama`a, da yawaita nafilfili da yin sallar Tuhajjid da yawaita karatun Alkur`ni da jin tafsirinsa da taimakon juna da ziyarar `yan uwa da mararsa lafiya, kai har da zuwa aikin Umrah da aka fi kwadaita yinta a cikin watan na azumi, koda yake lokaci ya zo saboda halin kuncin rayuwa da al`umma suke ciki, Maluma da dama yanzu suna ta wa`azantar da masu hali da suke ta maimaita aikin Umran da su sadaukar da kudaden da za su kashe a zuwa Umrah wajen tallafa wa, abin da suka ce ya fi lada a wurin Allah.
Kamar yadda kanun makalar tawa ya nuna, aniyata in yi tsokaci ga masu fama da ciwon sukari da yadda za su iya tafiyar da jikinsu a cikin wannan wata mai alfarma, ta yadda zas u samu sukunin samun garabasar ladar dake cikin watan na Ramadan.Kamar yadda na ji daga wasu `yan kungiyar masu tallafa wa masu wannan cuta na jihar Kano wato Dokta Aminu Da`u, Likita mai kula da cututtukan da ba su yaduwa (irinsu ciwon na sukari), na Ma`aikatar Kiwon Lafiya ta jihar Kano da kuma Hajiya Dije Sule Kabara kwararriya a kan fannin girke-girke ababban assibiti na Sa Muhammadu Sanusi da ke `Yankaba kewayen birnin Kano.Sun gabatar a wata lacca ga masu cutar ta sukari a asibitin kwararru na Murtala da ke cikin birnin Kano a ranar Lahadin da ta gabata da kuma tattaunawar da muka yi da su a shirin BARKA DA HANTSI na gidan Radiyon Freedom da ke Kano kashe gari Litinin.
A cikin shirin na BARKA DA HANTSI jami`an biyu, sun bayyana cutar ta sukari a zaman nau`i uku, akwai ta daya da ake Type 1 da ta biyu da ake kira Type 2, sai kuma wadda takan kama mata masu juna biyu, wadda takan warke da zarar sun haihu. Masanan sun tabbatar da cewa akwai mutane sama da miliyan 282, a duniya da suke fama da wannan cuta, kuma an kiyasta cewa nan da shekarar 20, masu zuwa wato 2035, masu fama da wannan cuta a duniya za su iya kai miliyan 592. A kasar nan kuma an kiyasta akwai mutane miliyan 8 zuwa miliyan 12 masu fama da wannan cuta wadda akasari Type 2 (wadda ita aka fi fama da ita a duniya). Masanan sun bayyana cewa gaja aikin wata Na`ura da ke cikin cikin mutum da take sarrafa dukkan irin nauyin sukarin da ke cikin cikin mutum din.
Lalacewar wannan na`ura da masana kiwon lafiya suka ce akasari daga Allah (SWT) takan faru kan sanya mai ciwon na sukari ya shiga taka-tsan-tsan a kan abin da zai ci ko ya sha, duk da yake yana iya cin dukkan irin nau’in abincin da mai lafiya zai iya ci, amma da sharadin idan nau’in hatsi ne da akan surfa, irin su dawa da gero da masara da makamantansu, to zai iya cinsu ba tare da an yi surfen su ba wato datsa, koda kuwa kununsu zai sha. Haka zai iya cin dangin su doya da dankali da wake da acca da alkama da taliya da makaroni da kus-kus da makamantansu, da ba su bukatar surfawa, amma lalle ya rika hada dukkan abin da zai ci da nau’in ganyayyaki.
Alal misali ana bukatar mai ciwon na suga ya kasa abincinsa kashi uku, masu ba da karfin jiki irin su hatsi da doya ya ci kashi biyu cikin biyar.Kayayyakin lambu irin su abarba da gwanda da lemo da ayaba da ganyayyaki, su ma su rika zama kashi biyu cikin biyar na abincinsa.Sauran kashi dayan su zama masu gina jiki, irin su kwai da nama da kifi da madara da gyada da makamantansu. Ma`ana dai lalle mai ciwon na sukari ya kiyayi zaunawa ya take cikinsa da nau’in irin wadannan kayayyakin abinci da na ambata, a lokacin azumi ne ko ba a lokacin azumi ba, sannan ya kula da shan maganinsa da kuma motsa jiki.
A lokacin azumi sai ya kara kulawa da wadannan ka`idoji da masana kiwon lafiyar suka bayyana. Lalle ya rika jinkira sahur, ya kuma yi sahur da nau’in abinci mai gina jiki.Ya kuma kiyayi take cikinsa da dukkan abin da ya samu (wanda dama sunnar Manzo SAW ta yi hani da hakan). Da rana ya guji yin zirga-zirga cikin rana. Idan ya zo yin buda baki ya fara da `ya`yan itatuwa irin su dabino, kar ya wuce daya ko uku, lemon fata kar ya wuce biyu, ayaba kar ya wuce kwaya daya, kankana kar ya wuce ta N50.00k, abarba ma kar ta kai ta haka nan, ba kuma gaba daya zai sa su gaba ya shanye ba a lokaci guda, ko ya ce a yi masa hadinsu gaba daya da ake kira Salad din `ya`yan itatuwa. Idan ya zo cin abinci bayan buda baki sai ya ci da kula, kar kuma ya ci nama ko abinci mai-mai da yawa, haka ma shan ruwa mai sanyi,daidai yadda zai iya zuwa tarawu ko ya dan taka ya guji kwanciya duk irin lalacin da ya ke ji. Lalle idan har mai azumi ya ji ba ya iya yin azumi, to, ya yi kokarin saduwa da Likitansa, don neman dauki. Allah ya sa mu dace, mu zama muna daga cikin wadanda Allah zai `yanta daga wuta a cikin wannan wata mai alfarma amin summa amin.