Wani kamfanin suttura a kasar Japan ya fara dinka wasu riguna masu dauke da fankoki a jikinsu da za a rika sanya wa karnuka da maguna saboda tsananin zafin da kasar ke fama da shi.
Rigar dai na dauke ne da fankar da ke amfani da batir wajen yin caji wacce za ta rika busa wa dabbobin iska a sassan jikinsu.
- Ukraine ta kashe sojojin Rasha 100 da tankunan yaki a Kherson
- Ya kamata a debi matasa miliyan 5 aikin dan sanda — Basaraken Iwo ga Buhari
A cewar shugabar kamfanin Sweet Mummy wanda yake dinka kayan, Rei Uzawa, ta yanke shawarar kirkiro rigar ce bayan ganin yadda karenta mai suna Chihuahua ke fama da zafin ranar a duk lokacin da yake tafiya a kasa.
“Kusan kamar ma ba a yi damina ba a bana, dalilin da ya sa zafin ya zo da wuri ke nan, saboda haka wannan hajar da muka kirkira za ta dace da yanayin da ake ciki,” inji ta.
Tun bayan daukewar ruwan sama a karshen watan Yuni, Tokyo, babban birnin kasar ke fama da yanayin mafi tsanani a tarihi wanda ya kan kai kusan mataki na 35 a ma’aununin celsius.
A cewar Mami Kumamoto, wata mata mai shekarar 48, “Nakan yi amfani da kankara wajen sanyaya jikin karnukana, amma yanzu ina tunanin wannan fankar za ta taimaka musu ainun.”
Rigar dai wacce aka fara kirkira a farkon watan Yuli, akalla mutum 100 ne suka fara sayenta a tashin farko inji Rei Uzawa.
Bugu da kari, an dinka ta ne a girma daban-daban, kuma za a rika sayar da ita ne a Dalar Amurka 75, kwatankwacin kusan Naira 40,000.