✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tsananin kishi’

Hamida da Kausar Gimbiyoyi ne a masarautar Kaho inda mahaifinsu shi ne sarki a garin. Hamida ita ce babba a kan Kausar. Baki daya sun…

Hamida da Kausar Gimbiyoyi ne a masarautar Kaho inda mahaifinsu shi ne sarki a garin. Hamida ita ce babba a kan Kausar. Baki daya sun isa aure amma sarki ya ce yafi son aurar da babbar ’yarsa kafin karamar. Akwai wani Yarima wanda kauyensu ke makwabtaka da garin Kaho ya yanke shawarar auran daya daga cikin wadannan ‘ya’yan sarki.

Labari ya isa garin Kaho nan take aka shirya tarbar dan Sarki da kide-kide da bushe-bushe da sauransu.  Nan Hamida ta caba kwalliya don ta burge Yarima don ya aure ta amma hankalin Yarima sai ya koma kan Kausar wacce ba ta yi wata kwalliya a zo a gani kamar Hamida ba.

Daga nan Yarima ya shaida wa Sarki shi Kausar yake son a daura musu aure.  Ai nan fa hankalin Hamida sai ta yanke shawarar kashe kanwatrta Kaursa inda ta tura ta cikin wani kogi bayan ta hallaka ta.

Ashe wani makadi yana labe duk ya ga abin da ta faru.  Ana cikin haka sai aka gano gawar Kausar kuma aka yi mata jana’iza.  Bayan kura ta lafa ne sai Yarima ya yanke shawarar ya auri Hamida.

Ana cikin shagalin biki kafin a daura aure sai ga makadin ya halarci wajen bikin, da fara kada gangarsa sai aka ji muryar Kausar tana fadin Hamida ce ta kashe ta don ta auri Yarima.  Nan take Yarima ya fasa auren Hamida, inda ita kuma ta samu tabin hankali ta shiga cikin daji daga nan ba a sake jin duriyarta ba, ita ma ta halaka.

Manyan gobe darasin wannan labari shi ne babu kyau a rika yin tsananin kishi musamman ga mata.