✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin Bukola Saraki da Bola Tinibu

Rikicin Bukola da Bola yana neman mamaye harkokin gwamnati bacin rabuwar kai na ’yan jam’iyyarsu ta APC. Babban hadarin shi ne da ake danganta rikicin…

Rikicin Bukola da Bola yana neman mamaye harkokin gwamnati bacin rabuwar kai na ’yan jam’iyyarsu ta APC. Babban hadarin shi ne da ake danganta rikicin da Fadar Shugaban kasa da Majalisar dattijai, wanda hakan zai shafi dukkan ‘yan Najeriya da harkokin yau da kullum. Bayanai da suke fitowa daga bakunan makusantan masu rikicin, ya nuna cewa, shi wannan rikici ya samo asali ne tun lokacin da aka bai wa Bola Ahmad Tinibu damar ya kawo wanda zai zama mataimakin dan takarar Shugaban kasa, Bola Tinibu ya gabatar da kansa a kan shi ne zai zama mataimakin dan takarar shugaban kasar, inda shi Bukola Saraki ya nuna rashin goyon baya, ya kafa hujja da kasancewar dan takarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari Musulmi ne, idan aka hada shi da Bola Ahmad Tinibu, wanda shi ma Musulmi ne da kyar za su ci zabe, ganin yadda Jonathan ya yi agar bisa daurin gindin Kiristoci da raunanan Musulmi.
Shi kuma Ahmad Bola Tinibu maimakon wannan magana ta zaburar da shi, kasancewar kabilarsa ta Yarabawa kusan tamanin cikin dari (80%) ko fiye duk Musulmi ne, fiye da saba’in cikin dari 70% na adadin ‘yan Najeriya duk Musulmi ne. Wani babban misali shi ne, Muhamamdu Buhari da Tunde Idiagbon bacin dukkansu Musulmi ne, dukkansu kuma ‘Yan Arewa ne. Idan ma wasu jahilai sun yi tunanin don kasancewarsu sojoji a lokacin, sai mu tuna da zaben Alhaji M.K.O. Abiola da Alhaji Baba Gana Kingibe dukkansu Musulmi ne, aka zabe su, zaben da ba a taba yin zabe mai inganci da rinjaye kamarsa ba.
Duk Kiristocin Najeriya da na duniya suka goyi baya, soke zaben ba shi da alaka da Musuluncin sai nufaka da kiyayyar Musuluncin da burin wanda ya soke zaben  ya ci gaba da mulki babu ranar dainawa, wanda hakan ya jefa Najeriya cikin mummunan hali, bacin an kori wanda ya soke zaben a wulakance aka yi ta dambarwa har takai ga mutuwar wanda ya ci zaben Alhaji M.K.O Abiola a kurkuku.
Wasu saida suka yi gudun hijira saboda rikicin soke zaben. Shi  kansa Bola Ahmad Tinibu yana cikin wadanda suka yi gudun hijira, nima da iri-irina da muka fara yin rigima tunda aka yi wa Buhari da Idiagbon juyin mulki ba mu daina ba sai ma kara kaimi da muka yi, har takai ga an kakkama mu da tsare mu. Idan ba a manta ba, saboda ganin yadda aka yi adawa da soke zaben Abiola da Kingibe duk kasar baki daya,  har da wasu kasashen duniya da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa. Wanda ya soke zaben ya dauko kabilar Abiola, Enest Shonekan ya ba shi rikon mulkin kafin ya sauka, wanda bai karbu ba, a wajen abokan wanda ya kawo shi, suka kawar da shi, Sani Abacha ya hau.
 Shi ma aka yi ta fafatawa da shi har ya mutu, aka dauko wani kabilar Abiola- Olusegun Obasanjo daga kurkuku aka kakaba mana shi, akan zababben Shugaban kasa. Shi ma dai bai karbu a wurin Shugabannin Yarbawa ba, sai da aka kai ruwa rana, yayin da wadanda suka kakaba mana shi suka yi kararsa wurin Shugabannin Yarabawa da babban Lauya Rotimi Williams a kan wai sun yi da shi Obasanjo shekaru hudu zai yi ya ba su mulki, amma yake nuna ba zai ba su ba. Har Shugaban Yarabawan Abraham Adesanya da Rotimi Williams suka kira Obasanjo don su ji ta bakinsa, Olusegun Obasanjo bacin ya jawo hankalinsu a kan Kundin Tsarin Mulki, wanda ya bai wa Shugaban kasa damar idan ya kammala zangon farko zai iya neman ya ci gaba da zango na biyu. Sannan ya yi musu cikakken bayani kan yadda ya bar mulki 1979, ya koma 1999 shekaru 20, ya tarar an sace dukiyar kasar karkaf har an ciyo bashin IMF na fiye da Dala Biliyan Talatin da Uku (US$33bn).
Bacin an rusa komai, shine suka fara bashi hadin kai wajen kwato abin da aka sace –  ta yin amfani da EFCC. Har Obasanjo ya gama tsakaninsu da Bola Tinibu babu shiri, kamata ya yi Bola Tinibu ya tuna Obasanjo ne kurum ya ce bai yarda Musulmi biyu su shugabanci Najeriya ba a matsayin Shugaban kasa da Mataimakin Shugaban Kasa, ba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba. Shi ma Bukola Saraki wajen Obasanjo ya ji ba a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya gani ba.
Koma dai mene ne bai kamata mu bari rikicin Tinubu da Bukola Saraki ya zama sanadin rushewar gwamnati ba, tunda nike mu ne, zunzurutunmu muka hadu muka zabi wannan gwamnati, kaddara tasa ba mu ne za mu gudanar da gwamnatin ba, sai su saboda matsayinsu a jam’iyyunsu da suka hadu suka zama APC har suke ganin idan suka rusa APC su suna da makoma. Saboda haka nike jawo hankalin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ko ta kwana. Ya nemi mutane na kwarai ba masu kowanne irin laifi ba, yadda canjin da muke bukata zai samu ya kuma dore. Haka nake jawo hankalin ‘yan’uwana da aka zalunta, aka yi wa sata, aka kasha wa ‘yan uwa da wadanda ake sacewa ‘yan’uwa, mu yi taka tsantsan da yadda ake yi wa gwamnati zagon kasa, kada mu jingina laifin kan Buhari don shi ne Shugaban kasa. Mu yi duk abin da za mu  iya yi na taimakawa kada su yi uwar-watsi su mayar da mu gidan jiya- Allah ya kiyaye.
Alhaji Abdulkarim Daiyab, shi ne  Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,  Tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (A.D) na Kasa baki daya,  Tsohon Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu, Da Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA).