✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar fetur: Gwamnati za ta fara mayar wa jama’a motocinsu su koma amfani da Gas

NITT ta ce za ta yi hakan ne saboda tsadar man fetur

Cibiyar Koyar da Fasahar Sufuri ta Najeriya (NITT), ta ce za ta fara canza wa jama’a motoci masu amfani da man fetur su koma amfani da Gas, sakamakon tsadar fetur din.

Shugaban cibiyar, Dokta Bayero Salih-Farah, ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar cibiyar da ke Zariya, a Jihar Kaduna.

Ya ce cibiyar za ta fara gudanar da aikin ne a ofisoshinta da ke dukkan shiyyoyin siyasa guda shida da ke kasar nan.

Dokta Bayero ya kuma kara da cewa, makarantar ta fara wannan gagarumin shiri tun kimanin shekarar da ta gabata, kuma za ta shirya tarukan horaswa a sassan kasar nan a makonni uku masu zuwa domin fara aiwatar da aikin gadan-gadan.

Kazalika ya ce Gas nada matukar sauki fiye da fetur a halin yanzu, wanda ’yan Nigeria za su samu sauki wajen kashe kudade da zaran sun sauya ababen hawan nasu daga amfani da fetur zuwa gas.

Daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su dauki wannan dama wurin bayar da hadin kai don samun nasarar shirin.