Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji.
Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya.
- An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe
- Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta
Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu.
Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma suka yi tafiya za su iya kama tashar a shafinta na intanet a https://trustradio.com.ng ko a manhajar Radio Garden.
Haka kuma za a iya saurarenta shafukan Aminiya da Daily Trust da shafukan sada zumunta.
Da zarar tashar ta kammala gwajin za ta fara watsa ƙayatattun shirye-shirye da labarai tare da rahotanni masu ilimantarwa, faxakarwa tare da nishaɗantarwa.