✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya aminta a fara shirin mika wa Joe Biden mulki

Bayan makonni uku da shan kaye a zaben Amurka da aka gudanar, Shugaba Donald Trump ya saki kari inda ya amince a yi duk wata…

Bayan makonni uku da shan kaye a zaben Amurka da aka gudanar, Shugaba Donald Trump ya saki kari inda ya amince a yi duk wata mai yiwuwa ta fara shirin mika mulki ga zababben Shugaba Joe Biden.

Cikin wani sako da Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya nemi hukumomin gwamnatin kasar a hukamance su dirfafi shirin mika mulki yayin da ya ke bayar da tabbaci a kan cewa har yanzu yana nan a kan bakansa ta ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben.

Da wannan ne Hukumar da ke kula da ayyukan gwamnati a Amurka (GSA), ta bayar da izini ga zababben shugaba Joe Biden kan cewa zai iya fara shirin karbar gwamnati kamar yadda doka ta bashi dama.

Shugabar GSA Emily Murphy ce ta sanar da hakan cikin wata wasika da ta aike wa Joe Biden, tare da cewa ta yi hakan ne bisa la’akari da dokokin kasar kuma babu wanda ya yi mata katsalandan.

Tun gabanin karbar mulki, Shugabannin Hukumomin kasashen Turai biyu sun gana da zababben shugaban Amurka, inda suka gabatar masa da goron gayyatar wani taro na musamman da za a gudanar a badi a birnin Brussels na kasar Belgium.

Shugaban Majalisar Turai Charlse Michel da Shugaban Gudanarwa Ursula von der Leyen sun bayyana aniyarsu ta aiki tare da Biden domin dinke duk wata Baraka da aka samu tsakanin Yankin da Amurka a karkashin jagorancin Donald Trump.