Bayan rasuwar marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a ranar Lahadi 20 ga Satumba2020, masu zaben sarki na Masarautar Zazzau sun fara zama don zaben wanda zai gaji marigayi Sarkin ne a ranar Alhamis 24 ga Satumba.
A ranar wasu majiyoyin da suke kusa da masu zaben Sarkin sun shaida wa Aminiya cewa masu zaben Sarki sun fara tantance masu son hawa gadon sarutar sai dai da wuya su cimma matsaya, amma suna sa ran zuwa Juma’a 25 ga Satumba su cimma matsaya tare da mika wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i sunan mutum uku daga cikin biyar da aka ce suna sahun gaba a cikin masu neman sarautar.
Wadanda suka fafata a neman gadon sarautar sun fito ne daga gidaje uku daga cikin hudu, wato gidajen Katsinawa da Barebari da Mallawa, yayin da gida na hudu wato na Sullubawa ba su bayar da sunan kowa ba.
A yayin takarar mutum bakwai ne suka nemi kujerar sarautar bibbiyu daga gidajen Bare-bari da Mallawa, sai na bakwai daga Gidan Katsinawa da suka hada da Iya da Turaki da Uban Gari da Dan Galadima da Sarkin Kudu.
Amma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa iyalan marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris, sun amince Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris ya wakilci gidansu a neman sarautar saboda shi ne babba.
A Gidan Barebari, Alhaji Mannir Jafaru Hakimin Basawa ne kadai ya fito takarar, inda Aminiya ta samu labarin cewa babu wata jayayya da ta fito fili a tsakanin gidansu.
A gidan Mallawa kuma wadanda suka fito takara su ne Magajin Garin Zazzau, (yanzu Sarkin Zazzau), Alhaji Ahmadu Nuhu Bamalli da Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya da Barden Kudun Zazzau, Alhaji Hassan Tijjani.
Masu zaben Sarki sun kada kuri’a
Masu zaben sarki da suka hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Makama Karami, Alhaji Muhammad Abbas da Fagachin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad da Limamin Juma’a, Malam Dalhatu Kasim da Limamin Kona, Malam Muhammad Aliyu sun kada kuri’ar zaben sabon Sarkin a ranar Alhamis da daddare.
An gudanar da zaben ne a gaban Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma’aikata da Kwamishinan ’Yan sanda da sauransu.
Kuma bayanai sun ce an bi dukkannin ka’idojin da aka tsara na zaben sabon sarkin, inda rahotanni suka ce uku daga cikin sarakuna karagar sun zabi Iyan Zazzau Alhaji Bashari Aminu, kwararren akanta, dan kasuwa kuma hakimi mafi dadewa a cikin masu neman.
Turakin Zazzau Alhaji Aminu Idris da Yariman Zazzau, Alhaji Mannir Ja’afaru kuma sun samu kuri’a daidaya.
Masu zaben Sarkin sun mika wa gwamnati rahotonsu a washegari Juma’a da rana don Gwamna El-Rufa’i ya zabi daya daga cikin mutum uku da suka mika masa.
Sunayen da suka mika “Don amincewa da daukar mataki na gaba” sun hada da Bashir Aminu da Aminu Idris da kuma Mannir Ja’afaru.
Sai dai bayan kwanaki ana jiran sanarwar nada sabon Sarkin ne sai Gwamna El-Rufai ya soke zaben, inda a ranar Laraba 30 ga Satumba, 2020, ya bayar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewa ya soke zaben ne saboda an cire sunayen wadansu mutum biyu da suke son sarautar.
Ya fadi cewa gwamnatin jihar ta umarci masu zaben Sarkin su sake tantance mutum 11 da suke son sarautar da suka hada da Bashir Aminu (Iyan Zazzau) da Aminu Shehu Idris (Turakin Zazzau) da Muhammadu Munir Ja’afaru (Yariman Zazzau) da Ahmad Nuhu Bammali (Magajin Garin Zazzau) da Abdulkarim Aminu (Wamban Zazzau) da Aminu Umaru Idris (Dangaladiman Zazzau).
Sauran su ne Bello Umaru Idris (Baraden Zazzau) da Saidu Mailafiya (Ciroman Zazzau) da Shitu Dikko (Dangaladiman Waziri Zazzau) da Sambo Shehu Idris (Sarkin Kudun Zazzau) da kuma Yusuf Shehu Idris (Sadaukin Zazzau).
Sai dai a daidai wancan lokacin daya daga cikin ’ya’yan marigayi Sarkin Zazzau din wanda aka ambaci sunansa a cikin masu neman sarautar da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa babu mai neman sarautar a cikinsu in baya ga Turakin Zazzau Alhaji Aminu Shehu Idris, don haka ba su da hannu a sunayen da ake cewa suna neman sarautar.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa Gwamna El-Rufai ya yi ta jan kafa kan batun ne saboda babu sunan ko daya daga cikin wadanda yake so ya nada a sarautar.
Majiyar ta ce zaben da masu zaben sarki suka yi an yi shi cikin gaskiya da amana a gaban manyan jami’an da aka ambata a sama, kuma an yi zagaye uku ana gudanar da zaben a gabansu kafin masu zaben sarkin su yi waje da mutum 8 su zabi ukun, kuma bayan haka ne Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abbas Lawal ya kira Gwamnan ya sanar masa sakamakon.
Majiyar ta ce an sake umartar su kan su sake zaben amma sakamakon ya zamo daya, inda Sakataren Gwamnatin ya sake fita ya kira Gwamnan a waya ya shaida masa cewa an sake zaben amma sakamakon yana nan yadda yake.
Bisa yadda suka tantancen, Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu ya samu maki 88, sai Yariman Zazzau, Munir Ja’afaru ya samu maki 87, sai Turakin Zazzau, Aminu Shehu Idris ya samu maki 53.
Gwamnati ta bukaci Masu Zaben Sarki su sake zabe
Bayan sun mika sunan mutum uku din, sai Gwamnatin Jihar Kaduna ta tambaye su dalilin da suka yi watsi da sauran mutum takwas da suka nemi sarautar.
Sai ta bukaci da su sake zama domin yin sabon zabe tare da kara mutum biyu da sukan hada da Mai shari’a Tanimu Zailani da Alhaji Mu’azu Aliyu Ahmed ya zama mutum 13 ke neman sarautar.
Bayanai sun ce kafin nan gwamnatin ta mika sunayen mutum 11 ga hukumomin tsaro su tantance su maimakon mutum uku da suka tsallake siradin zaben farkon.
Daga cikin dalilan da gwamnati ta bayar na bukatar a sake zaben, akwai cewa an tantance biyu daga cikin masu neman sarautar guda biyu a zaman farko ba tare da ganin takardar bayanansu ba.
Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Jihar Kaduna, Muyiwa Adeyeye ya fitar ta ce, “Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna da Gwamnatin Jihar Kaduna sun bukaci a sake sabon zabe bayan yin watsi da na farkon da aka yi, inda aka yi ba tare da mutum biyu da suke da sha’awwa ba”.
Sanarwar ta kara da cewa, “daga cikin mutum 13 ne za a tantance, sannan a mika wa Gwamna domin ya zabi daya”.
Gwamna ya jingine zabin masu Zaben Sarki
Sai dai a ranar Asabar 3 ga Oktoba, Gwamnan ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na facebook cewa: “Yayin da nake jiran duba rahoton masu zaben sarki daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi, ina karanta littafina na uku kuma na karshe kan hanyar da ake zaben sarakunan: wato littafin Dokta Hamid Bobboyi mai suna “Ka’idojin Shugabanci a Bisa Koyarwar Wadanda suka Kafa Daular Sakkwato (Principles of Leadership According to the Founding Fathers of the Sokoto Caliphate)”.
“Shawarwarin Ma’aikatar da Rahoton Tsaro kan ’yan takarar ne za a turo mini don yanke hukunci na karshe.
“Don haka ku ci gaba da yi min addu’a in zabi Sarkin da zai tafiyar da Masarautar Zazzau ta bunkasa a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen karni na 21”.
Jita-jitar ‘a yaga’ ga masarautar
A ranar Talata ce aka wayi gari da jita-jitar da ke cewa Gwamna Nasir El-Rufa’i yana yunkurin yi wa Masarautar Zazzau a yaga, bayan da ya gaza samun amincewar Majalisar Masu Zaben Sarkin wajen sanya sunan Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a cikin sunaye ukun da suka kamata a mika masa.
Wannan jita-jita ta zo ne a daidai lokacin da jama’a suka kosa a nada sabon Sarkin Zazzau din.
Sai dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wannan jita-jita, inda ta ce batun sake fasali da gyaran masarautun ya faro ne tun shekara uku da suka gabata.
Ya nada kawunsa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau na 19
Bayan da Gwamna Nasir El-Rufa’i ya gaza samun shigar da sunan Ambasada Nuhu Bamalli a cikin sunayen mutum uku da masu zaben Sarki suka zaba ne, kwatsam a ranar Laraba 7 ga Oktoba, 2020, ya yi amfani da karfin ikonsa ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli wanda ake zargin kawunsa ne a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19.
Sanarwar nadin sabon Sarki ta fito ne daga Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kaduna, Alhaji Jafaru Ibrahim Sani wadda har wa yau take dauke da sa hannunsa.
Sanarwar ta ambato Gwamna El-Rufa’i yana taya sabon Sarkin murna tare da yi masa fatar gudanar da shugabanci nagari a zamaninsa.
Sabon Sarki Ahmed Nuhu Bamalli
An haifi sabon Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (tsohon Magajin Garin Zazzau) ne ranar 8 ga Yunin 1966, ya fito daga Gidan Sarauta na Mallawa.
Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli dan Magajin Garin Zazzau marigayi Alhaji Nuhu Bamalli dan Malam Yero Autan dan Abubakar Dardau dan Malam Musa Bamalli.
Ya samu digirinsa na farko a bangaren Lauya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1989, sannan ya yi digiri na biyu a Harkokin Kasashe da Diflomasiya a shekarar 2002 a dai wannan jami’a.
Sannan ya yi diplomar kwarewa kan Gudanarwa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu a 1998.
Ya kuma yi kwas kan magance rikice-rikice a Jami’ar New York da ke Amurka a shekarar 2009 da kuma Diploma kan tsara shugabanci a a Jami’ar Oxford da ke Ingila ashekarar 2015.
Babban mamba ne a cibiyar Chevening inda yake da kwarewar aiki ta shekara 26 a harkar banki da shugabanci da tarho da manasa’antu.
Kuma ya yi karatu a fitacciyar makarantar nan ta harkokin kasuwanci ta Harvard inda ya samu takardar shaida ta GMP a shekarar 2011.
Kafin nada shi a Sarkin Zazzau yana rike da sarautar Magajin Garin Zazzau (mutum na biyu mafi girma a sarautar ’ya’yan Sarki a Masarautar Zazzau).
Yana da mace daya Hajiya Mairo A. Bamalli da ’ya’ya biyar namiji daya da mata hudu.
Wakilici a kungiyoyin kwararru
- Wakili a Institute of Credit Administration (ICA)
- Wakili a Institute of Directors (MIOD)
- Wakili a Institute of Corporate Administrators (ICAD)
- Wakili a Institute of Facility Managers (IFM).
Sabon Sarkin mutum ne mai sha’awar hawan doki
Ambasada Nuhu Bamalli ya zama Sarkin Zazzau ne bayan shekara 100 rabon gidansu da sarauta
Allah ne Yake ba wanda Ya so mulki – Sabon Sarkin Zazzau
Jim kadan bayan sanar da shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya bayyana godiyarsa ga Allah, inda ya yi alkawarin gudanar da mulki mai kyau.
“Alhamdulilla. Bayan shekara 100 da barin sarautar Zazzau daga gidanmu, yau ta dawo. Allah ne Yake ba da mulki da wanda Ya so. Yanzu mulkina ya fara. Zan yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da gaskiya da amana. Allah Ya taimake mu baki daya, amin”, Sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Nuhu Bamalli ya sanar a shafinsa na Twitter.
Gidan Mallawa ya rabu da sarautar Zazzau ne kimanin shekara 100, tun rasuwar Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi a 1920.
Masu zaben Sarki sun yi mubayi’a
Duk da tirka-tirkar da aka samu kan zaben Sarkin da kuma jingine zabin masu zaben Sarkin, masu zaben Sarkin da suka hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Makama Karami, Alhaji Mahmud Abba da Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Mahmud da Limamin Jumaa’a Sheikh Dalhatu Kasim da Limamin Kona Sheikh Sani Aliyu dukkansu sun je sun yi mabayi’a ga sabon Sarki Ahmad Nuhu Bamalli.
Dole mu amince da zabin Allah – Yariman Zazzau
Da yake bayanin bayan nada sabon Sarkin Zazzau, daya daga cikin wadanda suka nemi sarautar, kuma yake cikin mutum uku da Masu Zaben Sarki suka zaba, Yariman Zazzau, Alhaji Muhammad Munnir Jafaru cewa ya yi, “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ina mai matukar godiya ga Allah (SWT) bayan na samu labarin nada Magajin Garin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau, wanda Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya yi.
“Ya zama dole mu amince da zabin Allah sannan mu taya sabon Sarkin murna. Allah Ya yi masa jagora, Ya samar da zaman lafiya ga mutanenmu, amin”.
Ya kara da cewa “A madadina da iyalina da abokaina da masu yi mana fatar alheri, ina mai matukar godiya gare ku bisa yadda kuka nuna min kauna da addu’o’i a wannan lokaci. Muna matukar godiya. Allah Ya saka muku da alheri”.
Ra’ayin Zage-Zage kan nadin
Lokacin da Aminiya ta tuntubi mutanen Masarautar Zazzau a garin Zariya da Kaduna ra’ayi ya sha bamban dangane da nadin sabon Sarkin, inda wadansu suke cewa nadin wasa da hankalin jama’a ne wadansu kuma suke cewa zamani ne da kuma kaddara don haka ya kamata jama’a su rungumi kaddara.