✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tiren-taliya tukunyar dambu

  A makonni da suka ranta a na durwan-kolo, na ji Usainin -Babajo, maitaimakin Baban Burin-huriyya, inda ya baza wa duniya cewa, Gwamnatin Tarairayyar Haurobiyawa…

 

A makonni da suka ranta a na durwan-kolo, na ji Usainin -Babajo, maitaimakin Baban Burin-huriyya, inda ya baza wa duniya cewa, Gwamnatin Tarairayyar Haurobiyawa za ta kasafta damin Hauro tiren taliya madambaci, don dambacewa da tsilli-tsaillin matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a kwaraya. Kuma an yi shirin aiwatar da daukacin kwantiragin ayyukan da aka bijiro da su a shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, ta yadda ba za a rage wa masu kwashi-kwaraf ko da karafanfana ba. Kun ga ke nan daukacin damin Hauron da aka yi baje kolinsu za a kunduge su, don magance kwata ‘aika-aikatar kwantiragin farar giwa.’
Jaridar Dalilin taron-su, ta ranar sili da kwanciyar magirbi ga watan Noman-Baba, a shfinta na kartamin lauje da karamin lauje, ta fayyace yadda za a aiwatar da dimbin ayyuka raya kasa, da hana almundana da kashe mu karkasa, inda wakilin jaridar ya tuntubi wani masanin tsimi da tanadi daga Jam’in Jama’ar Jami’ar Bayan-kada, wanda ya doka dimbin misalan aika-aikar tsimi da ta’adi da aka sha tafkawa a shekarun da suka arce, musamman a zamanin mulkin mai dan boto da sanda jirge. Wannan masani ya bijiro da cewa:
“Al’amura za su kyautatu, sabanin yadda a da idan aka yi kasafin Hauro gashin balama, sai a karshe a karke da kashe Hauro dari karamin lauje malala gashin tunkiya ko dari kofar hanci malala gashin tunkiya. Sauran ayyuka kuwa, sai a sake cuso su a jaddawalin baje-kolin Hauro na badin badada.”
Masanin ya fadakar da al’umma cewa, kowane ofishin gwamnati da hukumomin da kwe a karkashin ma’aikatu za su gabatar da ayyukan a za su iya karkarewa a kowace shekara, ta yadda ba za a rage ko karfanfana a lalitar ma’aikatar ba, ballantan wasu su handame.
Ita kuwa jaridar Fanco, wadda ake jkarantawa cikin yaren Ingilishi, idan an kanga gilashi, an kuma murguda baki kamar ana cin kilishi, ta bijiro da batutuwan yadda mahukuntan Haurobiya ke aiki tukuru wajen ganin sun shawo kan zaman kashe fatari, tare da jinka wa masu fama da talalar talauci Hauro dubu babban lauje, don kada su zama ja-ni-talau.
Abinm da ya sanya na falle muku shafukan wadannan jartidu, shi ne, a ranar sili da babban lauje na watan Noman-Baba na hadu da mai sayar da kayan gwanjo, inda na sayi tufafin kariyar hunturu. Muna cikin ciniki, sai dattijon nan ya koka mini cewa, Baba ya tara damin Hauro ya ki jinka mana komai. Ni kuwa, sai na kwantar masa da hankali, cewa, Baban Burin-huriyya zai difara muku damin Hauro, inda na fake da hujjar Usainin-Babajo kan kasafin damin Hauro tiren-taliya tukunyar-dambu, musamman ma tabbacin da nike da shi cewa, za a kundume damin ne wajen aiwatar da ayyuka. Su kuwa miyagu masu kwalamar dukiya, sai in ce das u CIN-BIN-KWALAM!
Haurobiyawa ya kamata mu fasko cewa, jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ba su kauce ba, har sai da suka tatuke lalitar kasar nan, musamman ganin cewa, sun ci kasa a zaben shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje. Kuma sun jefa kasa cikin rudani, har yamutsin Haramta bobo da kwambon bokoko ya kusa kai ta kasa.
Yanzu kuwa da suka tabbatar ba su da wani katabus, sai suka haifar da ruguntsumin rudanin Biyan-fura wanda tuni ya zama na Biyan-furfura a Bayan-fara. Domin mafi yawan matasan da aka ingizo su, su yi wa Haurobiyawa ta’annati duk ba a haife su ba, sa’adda kasar nan ta fafata yakin basasa, a tsakanin alif sili manuniyar sama da manuniyar kasa da kwanciyar magirbi zuwa alif sili manuniyar kasa da kwanciyare magirbi da zagaye. Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare sa-in-sa ba, ya ce ta ‘man-kaza ba ta karko.’
Lallai lokaci ya yi da za mu tallafa wa gwamnati wajen ganin ta aiwatar da kasafin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, don hana ‘sama-da-fadi.’ Kuma jam’iyya mai maganin zogi da radungu, ya kamata ta fasko jirgin masu yi mata zagon kasa, wadanda ke yunkurin kassara manufofinta na inganta rayuwar al’umma, tare da hana almundana da kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Saboda haka nike roko kan lallai duba kwakyariyar Dano Mai-alaye, wanda ya kuntuga zuki-ta-malle kama-kare ka hada shi da zomo, cewa, wai an yi sabi zarce da damin Hauro karamin lauje da babban lauje gashin balama. Shi kuwa babban asusun Haurobiya ya tabbatar da cewa, wannan waskiya kawai aka sharata.
Masu koyon watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu a Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, kada mu dore da karbar Hauro dubu babban lauje da za a rika jinka wa matasa don kwance su daga sasarin talalar talauci. Wajibi ne kowa ya yunkura wajen fardar gayauna; kada a bar saura. Wanda duk ya iya ’yan sake-sake da dinke-dinke, hakki ne da rataya a kan mutum ya horar da dan uwansa. Mu fara rage yuawan masu zaman kashe fatari, tun kafin hukuma ta fito da nata tsarin.
A kullum dai na saba jadaddawa, cewa, mu yi limbu-limbu a cikin lambu; mu farde gayauna, don samar da kayan dundume kururu, kada a bar mu da  na-mujiya kuru-kuru. Wadanda suka samu shaidar kammala koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a daukacin farfajiyoyin Bobo da kwambon boko, su edaina jira kwadagon farar kwala, don kada su yi mana wala-wala a wajen neman kadago. Sannan akwai bukatar a bunkasa manhajar cibiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen litatttafai, ta yadda wadanda suka kammala yaki da juhala za su himmatu wajen tabbatar da adala.