Uban Jam’iyyar APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya goyi bayan Darakta-Janar din kwamitin yakin zabensa, Abdulmumin Jibrin Kofa, na ficewa daga jam’iyyar mai mulki.
Kofa, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar Mazabar Kiru/Bebeji ta Jihar Kano, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ne a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.
- An kama jagoran ’yan sa-kai da suka kai hari ana bikin sallah a Zamfara
- EFCC na binciken yadda ’yan siyasa ke samun kudin fom din takara —Bawa
Ana hasasehn Kofa zai sake fitowa neman takarar kujerar dan majalisa a babban zaben 2023, amma ya fuskanci kalubale daga shugabancin APC na Kano.
Kofa, ya ce nan ba da jimawa ba zai bayyana jam’iyyar da zai koma.
“Na yi wa APC duk abin da ya kamata kuma lokaci ya yi da zan kara gaba; Zan bayyana sabuwar jam’iyyata nan da sa’a 24 masu zuwa in sha Allah, zan fitar da sanarwa ta musamman,” kamar yadda Abdulmumin Jibrin Kofa ya wallafa.
Kofa ya gaza komawa majalisa ne bayan ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Aliyu Detti Yako I, bayan da shugabannin jam’iyyar APC a jihar suka kaurace wa zabar shi.
Rikicinsa na shugabancin APC a Kano ya samo asali ne tun a 2019, lokacin da aka dakatar da shi daga shiga harkokin siyasa a Karamar Hukumar Bebeji ta Kano.
Tun daga wancan lokaci Kofa ya samu koma baya a jam’iyyar duk da cewa yana taka rawar gani a tafiyar Bola Ahmed Tinubu da ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar.