✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ba da umarnin cafko wadanda suka kashe mutane 115 a Filato

Harin dai na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 115 a Filato.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su yi duk mai yiwuwa su cafko maharan da suka kashe mutane 115 a Jihar Filato.

A ranar jajibirin Kirsimeti ne ’yan bindiga suka kai farmaki a wasu yankuna sama da 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi suka kashe sama da mutum 115.

Maharan na ranar Lahadi sun kone gidaje akalla 200, suka sace kayan abinci, suka lalata dukiya mai tarin yawa; Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin hare-haren.

Tinubu ya yi tir da harin, sannan “ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta shiga yankin, su kuma kamo wadanda suka yi danyen aikin,“ in ji sanarwar da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar.

Sanarwar ta ce shugaban ya ba da umarnin tura kayan agaji yankin domin rage wa al’ummar radadin halin da suke ciki.

“Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Filato, tare da ba wa ’yan Najeriya tabbacin wa cewa wadanda suka yi wannan aika-aika ba za su tsira ba,” in ji Ajuri.

Hare-haren da aka fara a Bokkos sun fantsama zuwa Barkin-Ladi, inda aka gano gawarwakin mutane 30, a cewar shugaban Karamar Hukumar, Danjuma Dakil.

Gyang Bere, kakakin Gwamnan Caleb Mutfwang, ya ce “gwamnati za ta dauki matakan da suka dace don dakile hare-haren da ake kai wa al’umma.”

Kungiyar kare hakkin bil Adama, Amnesty International ta soki gwamnati kan hare-haren.

“Hukumomin Najeriya sun kasa kawo karshen munanan hare-hare a kauyukan Jihar Filato da wasu sassan Arewancin kasar,” in ji kungiyar a shafinta na X.

Arewa maso Yamma da Tsakiyar Najeriya sun dade suna fama da hare-haren ta’addancin ’yan bindiga musamman a kauyuka inda suke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.