Mai Martaba Sarkin Ibadan, Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun Alli Okunmade II, ya yi wa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Farfesa Hafsat Ganduje nadin sarauta.
Bikin nadin sarautar da aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo a ranar Asabar, ya samu halarci manyan baki ciki har da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
- Mun soma tattauna yiwuwar hadewa da Peter Obi —Kwankwaso
- Zaben Ekiti: SDP ta yi watsi da sakamako, za ta garzaya kotu
An yi wa Ganduje nadin sarautar Aare Fiwajoye na Ibadan yayin da aka nada mai dakinsa Yeye Aare Fiwajoye ta Ibadan.
Masarautar Ibadan wadda ta ce wannan nadi ba shi da wata nasaba da tarin dukiya, ta ce zai kara dankon zumunci tsakanin al’ummar Yarbawa da ke Kudancin kasar da kuma Hausawa da ke Arewa.
Da yake jawabi a wurin bikin, Tinubu ya ce wannan nadin sarauta zai kara inganta dangartakar da ke tsakanin garin Ibadan da Kano wanda a cewarsa su ne birane mafi dadewa a kasar nan.
A nasa jawabin, Ganduje ya bai wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa da kwadaita musu muhimmancin kulla alakar auratayya tsakanin kabilu, yana mai cewa hakan zai habaka zaman lafiya da hadin kai a kasar.
Sauran manyan baki da suka hakarci bikin sun hada da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu da sauransu.