More Podcasts
Shugabar Kungiyar Matasan Zaurawa ta Kasa reshen Jihar Kano, Hajiya Hafsat Ahmad Jingau ta bayyana cewa zaurawa na cikin kunci da tashin hankali.
Shugabar ta fadi haka ne a tattaunawarsu da abokin aikinmu Muhammad Auwal Sulaiman a cikin shirin Daga Laraba wanda sashin yada labarai ta intanet na Daily Trust ke shiryawa a kowane mako.
- ‘Noman Zabibi zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya’
- Jirgin saman Najeriya zai soma jigila a Afrilun badi — Hadi Sirika
Ta bayyana irin kalubalen da zaurawa ke fuskanta musamman idan an bar su da daukar dawainiyar ’ya’yansu bayan mutuwar aurensu ko rasuwar mazajensu.
Hajiya Hafsat ta kara da bayyana irin fadi-tashin da zaurawa da dama ke fuskanta a wannan hali na zawarci.
Ta ce, baya ga kalubalen rashin samun kulawa da zaurawan ke fama da ita, suna fuskantar barazana daga wurin maza masu zuwa neman aurensu, inda dama wasu ba da gaske suke ba, suna zuwa ne da wata manufa ta daban.
A karshe ta yi kira da matan aure da su ci gaba da hakuri da yanayin da suka tsinci kansu a gidajen mazajensu saboda babu wani abu mai dadi a cikin rayuwar zawarci sai wahala da tashin hankali.