Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce taron da gwamnonin PDP da suka yi ranar Litinin, bata lokaci ne kawai.
Hakan ya fito ne daga Sakataren Rikon Kwarya na APC, John Akpanudoedehe, a Abuja a ranar Litinin.
- An kama uba yana lalata da ’yar cikinsa
- Zan kawo hargisti a zaben 2023 — Igboho
- An kama mata da miji masu safarar jarirai
“Idan aka lura abin da gwamnonin PDP suka cimma a matsaya ba komai ba ne face bata lokaci,” a cewarsa.
Ya kara da cewa gwamnonin sun yi zaman kashe wando ne kawai, tun da a zaman nasu ba ta bullo da wata sahihiyar hanya don tallafawa yanayin da kasa ke ciki ba.
Ya ce, abun Allah wadai ne taron gwamnonin PDP da suka yi, domin sun fi mayar da hankali kan siyasa maimakon abin da suka yi ikirarin za su yi a wajen taron.
Kazalika, ya ce nasarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ta samu tun bayan darewarsa kan kujerar mulki a bayyane suke ba sai an fada ba.
A cewarsa, kowa ya san irin fadi-tashin da gwamnatin APC ke yi don tabbatar da saituwar komai a bangaren tsaro da abin da ya shafi rikicin manoma da makiyaya, amma maimakon gwamnonin PDP su zo a hada kai sai suka siyasantar da lamarin.
Ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewar, Gwamnatin Buhari za ta ci gaba da hada kai da daidaikun mutane da ke son ciyar da Najeriya gaba, wajen ganin an samu babban tagomashi.