✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihin Masarautar Potiskum

Sarakunan da suka mulki Masarautar Potiskum kamar yadda tarihi ya nuna sun kasu kashi biyar.

Potiskum da ke Jihar Yobe gari ne kwaya daya a Arewacin Najeriya da ke da sarakuna masu daraja ta daya guda biyu, wato Masarautar Fika da Masarautar Potiskum ta kabilar Ngizim (Gizimawa) da ke tutiyar ita ta kafa garin.

Sai dai akwai masu cewa, ba Potiskum ne hedikwatar Masarautar Gizimawa ba hedikwatarta tana Yarimaram ne da ke wajen garin Potiskum.

A tattaunawa da Aminiya Mukaddam na Masarautar Potiskum kuma tsohon Babban Sakatare a Jihar Yobe, Alhaji Lawan Usman Hassan ya bayyana tarihi da irin gwagwarmaya da kabilarsu ta Ngizimawa ta sha kafin kafa masarautar da yadda sunan na Potiskum ya samo asali daga harshensu na Ngizim:

Ranka ya dade, yaya tarihin Masarautar Potiskum yake?

Masarautar Potiskum masarauta ce mai dogon tarihi, kuma a duk yayin da za ka yi maganar masarauta to ya zama wajibi ka fara da tarihin mutanen masarautar tukunna.

Masarautar Potiskum kabilar Ngizim ko in ce Ngizimawa ne ke tattare da ita, kuma wani lokacin dalili ne ke sa a samu masarauta da iko har a kafa ta, don haka in ka fara maganar Potiskum dole ka yi maganar Ngizimawa wadanda suna daga cikin kabilun Jihar Yobe.

A wani tarihi ana ganin kamar kabilar Ngizim da Badawa ba a san daga inda suka taho ba, a nan suke, in an matsa bai wuce a ce daga inda Kaneem Borno take a wancan lokacin wato daga Gabas da Tafkin Chadi daga bisani suka dawo yamma da Tafkin Chadi, amma dai yadda tarihi ke nunawa Ngizimawa suna daga cikin kabilun da suka fi dadewa a nan yankin.

Akwai maganganu cewa, kabilarku ta Ngizimawa, kabila ce da ta fito daga Ngazargamu mece ce gaskiyar maganar?

Yauwa, kamar yadda na fada maka cewa wasu masana tarihi na cewa, wasu kabilun ba a san daga inda suka taho ba, in ma sun taho daga wani waje bai wuce tarihin da ke cewa, wasu kabilun sun taho ne daga wajejen Masar.

In ma haka ne sun fara zama ne a wasu wurare da ke cikin Chadi ta yanzu wadanda da su ne aka yi gwagwarmayar kafa Daular Borno a wancan lokaci, kuma a yanzu in ka je wajen Chadi za ka tarar da wani bangare Ngizimawa ne a wurin.

Domin a shekarun baya daya daga cikin sarakunansu ya zo nan ya kawo ziyara Masarautar Potiskum domin Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayaro shi ya ce masa bari zan hada ka da ’yan uwanka shi ya sa aka kawo shi nan wajen Mai Potiskum.

Don haka har yanzu akwai Ngizimawa a Chadi, kuma da suka ketaro suka yi wo yamma da Tafkin Chadi a wancan lokaci shi ne suka zo suka hadu da Daular Borno suka taho wajen Ngazargamu ta wajen Mawo don ka san suna daga cikin kabilun da aka yi gwagwarmaya da su, kuma wasu masana tarihi na cewa, ita kanta kalmar Ngazargamu tana da alaka da harshen Ngizim.

In ka taho Karni na 16 lokacin Mai Idris Alooma ne aka kafa Daular Ngazargamu lokacin akwai wani limaminsa Ahmed Ibn Fur’tua da ya rubuta wata takarda a kan yake-yaken Idris Alooma.

A cikin rubutun ya ba da labarin cewa, kalmar Ngizim akwai nau’o’in wannan suna wanda duk da cewa an bambanta su da alama suna nuna mutane iri daya ne Ngizim, Ngazar, N’kazzar, N’gujam, N’gissam.

A wani bangare na bayanansa ya nuna cewa, Mai Ali Ghaji Dunamani ne ya kafa birnin Daular Ngazargamu a shekara ta 1462.

To a nan ne zai ba ka ko su wane ne Ngizimawa.

A cewarsa akwai batun Ngizim sannan kabilar a yammacin masarautar da ake kira Binawa, Binawa kuma ana kiranta da Mabani wadda ta tashi daga yankin Bursari yamma da Ngazargamu zuwa wajejen Katagum a Jihar Bauchi ta yanzu, a cewarsa duka Ngizimawa ne.

Kuma daga Ngazargamu ya yi Kudu ma akwai Ngizimawa, amma daga baya suka juye bayan sun hade da Kanuri sai suka zama Kanuri, shi ne ake kiran su da Ngazar, su ne suke Gujba da Dawuura.

To ana cikin haka Idris Alooma ya samu matsala da su saboda wasu suna tare hanya wanda hakan ya sa suna kawo matsaloli a harkokin cinikayya hakan ya sa Idrissa Alooma ya dauki mataki a kansu aka ci wasu da yaki, wasu suka mika wuya, wasu kuma suka nausa Kudu cikin kungurmin daji.

To a haka ne ganin cewa zuwan Ngizimawa ayari-ayari sakamakon wannan yaki zuwa wannan yanki shi ne ake alakanta Ngizimawan da yankin na Potiskum wato garin Potiskum na yanzu.

Yallabai, yaya tarihin samuwar garin Potiskum a matsayin hedikwatar Masarautar Ngizim?

Abin da ya sa Potiskum ta zama hedikwatar Ngizim shi ne, Ngizim su ne suka kafa garin Potiskum babu ko tantama a kan haka, domin su ne suka assasa garin na Pataskum ko Potiskum inji Turawa.

To yallabai a ina ya samo asalin sunansa na Pataskum?

To lallai sunan Pataskum (Potiskum) kalma ce ta Ngizim yadda ya nuna ‘Pata’ na nufin daji yayin da ‘Sukum’ itacen Baushe ne kasancewar wannan itace yana da yawa a wannan yanki na Pataskum a wancan lokaci.

Don haka kalmar Pataskum ta samu ne daga kalmomin nan biyu na Ngizim wato PATA da SUKUM.

Yallabai, babu wata kabila da Ngizim suka samu a wurin ke nan lokacin da suka zo?

Lallai akwai, ba kuma akwai ba domin kusan lokaci daya suka zo Potiskum da kabilar Karekare duk da cewa kafin nan Karekare na zaune ne a wajen yankin Langawa a kan hanyar Kari daga garin na Potiskum da kuma yankin FAKARAU don haka tare Ngizim da Karekare suka zo garin Potiskum.

Don haka za a iya cewa Ngizimawa da Karekare kusan su ne kabilun da lokaci daya suka zo garin Potiskum shi ya sa akwai tarayya kwarai da gaske a tsakanin kabilun Ngizimawa da Karekare dangane da garin na Potiskum.

Kuma har ila yau a wajejen Karni na 19-20 karin wasu Ngizimawa sun taso yayin yake-yaken Fulani inda suka taho nan yankin Potiskum suka samu ’yan uwansu Ngizimawa da wasu Karekare.

Sun zo ne tare da BAUYA kuma sun taso ne daga Mugni sakamakon harin da mayakan Fulani na Jihadi suka kai wa Ngazargamu shi ne suka Dauki hanya ta bangaren Kudu zuwa Kaisala ind da isar su Bauya da ayarinsa suka taimaka wa mazauna Kaisala suka samu nasarar murkushe wani hari da Ngazar reshen Ngizim na Dawuura ya kawo musu.

To bayan kai wannan hari ne na Dawuura kasancewar kuma mayakan na Dawuura sukan farmaki mazauna garin Potiskum amma zuwan Bauya ya ci su da yaki daga bisani sai Bauya ya zo ya kafa nasa yankin da ake kira Pataskum wanda Turawa suka gurbata shi suka mayar da shi Potiskum a yanzu.

Lokacin da Bauya ya zo Pataskum ya tarar da wani shugaban ’yan hatsi a lokacin da ake kira da ‘Dugun Awu’ a lokacin shi ne jagora amma kuma na wasu jinsin masu sana’a ba dukkan mutane ba, don haka ne Bauya ya ci gaba da mulkar garin na Potiskum har zuwa wani lokaci.

Daga lokacin Sarki Bauya zuwa yau da Sarkin Potiskum Mai martaba Mai Umar Bubaram Ibn Wurya Bauya ke mulki sarakuna nawa Masarautar Potiskum ta yi?

Sarakunan da suka mulki Masarautar Potiskum kamar yadda tarihi ya nuna sun kasu kashi biyar ne ma’ana tun daga lokacin mulkin Daular Sefawa kawo yanzu. Sarakunan Masarautar Potiskum yayin mulkin Sefawa su 7 ne:

1. Sarki Mai Bauya, Shekara ta 1600

2. Sarki Awany ba a fadi shekaru ba.

3. Sarki Mai Dangari

4. Sarki Mai Dawi (Dow 1) 1824

5. Sarki Mai Darama (Kuma chi bai)

6. Sarki Mai Kele

7. Sarki Mai Malam Bundi 1 wanda ya rasu a 1835

Sarakunan Masarautar Potiskum lokacin Daular El-Kanemi 5 ne:

1. Sarki Mai Muzgai wanda El-Kanemi ya ba shi Kachalla saboda jarumtarsa ya yi mulkin Potiskum daga 1835-1856

2. Sarki Mai Jaji 1 daga 1856-1858

3. Sarki Mai Nejo daga 1858-1866

4. Sarki Mai Namiyanda (Numainda) 1866-1893

5. Sarki Mai Gabau (Gabbo) 1893-1902

Sarakunan Masarautar Potiskum lokacin Turawan Mulkin Mallaka 2 ne kafin dawwamar da mulkin ga Masarautar Fika su ne:

1. Sarki Mai Bundi II daga 1903-1909

2. Sarki Mai Agudum daga 1909-1913

To daga nan ne Turawan suka yi karfakarfa suka dauwamar da Masarautar Potiskum kacokan ga Masarautar Fika aka yi jerin sarakunan Potiskum kamar haka:

1. Sarki Mai Jaji na II daga 1913-1919

2. Sarki Mai Bongum 1919-1924

3. Sarki Mai Gankiyau 1924-1927

4. Sarki Mai Bundi na III 1927-1933

5. Sarki Mai Jaji III 1933 wanda wata 3 kacal ya yi a kan mulki

6. Sarki Bauya na II 1933-1984

7. Sarki Mai Shu’aibu 1984-1993

Sarakunan Potiskum bayan farfado da masarautar:

1. Sarki Mai Muhammad Atiyaye ya zama Sarkin Potiskum jim kadan bayan da Gwamna Bukar Abba Ibrahim ya sake farfado da martabar masarautar a 1993 da hedikwatarta a Yerimaram inda aka nada Mai Muhammad Atiyaye a ranar 5/08/1993, ya yi kwana 53 bisa mulki Allah (SWT) Ya karbi rayuwarsa.

2. Bayan da Mai Atiyaye ya rasu ne sai aka nada Sarki Mai Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya a 1993 zuwa 1995 gwamnatin soja ta wancan lokacin ta dakatar da masarautar.

3. Bayan dawowar mulkin farar hula aka yi dace Sanata Bukar Abba Ibrahim ya sake lashe kujerar Gwamnan Jihar Yobe sai ya sake dawo da Masarautar Potiskum karo na biyu a shekarar 2000 inda aka sake nada Mai martaba Mai Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya a matsayin Sarkin Masarautar Potiskum har zuwa yau.

Wannan shi ne ainihin tarihin Masarautar Potiskum da kabilar Ngizim (Ngizimawa) ke sarauta.

Kuma a yanzu muna zaman lafiya da kowa a wannan yanki da dukkan kabilun da muke tarayya da su.