Malam Aminu Kano shahararren ɗan siyasa ne da ya jagoranci gwagwarmayar neman ƴancin talakan Arewacin Najeriya tun daga zamanin mulkin mallaka har zuwa Jamhuriya ta Biyu.
Ko da yake bai kafa gwamnati a Jamhuriya ta Farko ba, ya ci nasarar koyawa talaka ‘na ƙi’.
A zamanin mulkin soja ya riƙe muƙamin minista inda ya ci gaba da wayar da kan al’ummar Arewa. Sai dai siyasa ta suɓuce masa a Jamhuriya ta Biyu, bayan da gwamnonin da suka yi nasara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyarsa suka yi masa tawaye.