✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Saba’in da Biyar:  Wanda ya hau teku domin yakin daukaka kalmar Allah:                       …

Babi na Saba’in da Biyar:  Wanda ya hau teku domin yakin daukaka kalmar Allah:                           

580. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Yahya daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Ummu Haram ta ba ni labari cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya fada a cikin dakinta lokacin da ya farka cikin barci alhali yana dariya, na ce: “Ya Manzon Allah! Me ya sanya ka dariya? Ya ce, “Na yi mamakin wadansu daga cikin al’ummata ne da za su hau teku kamar sarakuna bisa karagun (kujerun) sarautu.” Sai na ce: “Ya Manzon Allah! Ka roka mini Allah Ya sanya ni daga cikinsu.” Sai ya ce: “Ke kina daga cikinsu.” Sa’an nan ya sake barci ya farka yana dariya sai ya fada mini kamar yadda ya fada da farko. Haka ya faru har sau biyu ko sau uku, na ce: “Ya Manzon Allah!Ka roka mini Allah Ya sanya ni daga cikinsu.” Sai ya ce: “Lallai ke kina daga cikin jama’ar farko.” Sai ta yi aure da Ubbada dan Samit ya fita da ita zuwa yakin, lokacin da take komowa sai dokinta ya kayar da ita, lokacin da take kokarin hawa, ta fado wuyanta ya karye.”

Babi na Saba’in da Shida: Neman taimakon raunana da mutanen kwarai cikin yakin daukaka kalmar Allah. dan Abbas ya ce: “Abu Sufiyan ya fada mini cewa: “kaisar ya fada mini cewa: “Na tambaye ka, shin manyan mutane suke bin sa ko raunana? Ka ce, “Raunana ke bin sa, su ne kuwa mabiya manzanni.”

581. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Muhammad dan dalha daga dalha daga Mus’ab dan Sa’ad ya ce: “Sa’ad (danAbu Wakkas ) (Allah Ya yarda da shi), lallai shi ya nuna shi yana da fifita a kan wadansu. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Shin ko kun san ba domin raunananku da ba ba ku samun taimako (daga Allah) da arziki ba.”

582. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce, ya ji Jabir ya karbo daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda su) daga Annabi (SAW) ya ce: “Zamani zai zo jama’a za su fita zuwa yakin daukaka kalmar Allah, sai a rika cewa: Shin ko akwai wanda ya taba zama tare da Annabi (SAW)? A ce, “Na’am, sai a ci nasara.” Sa’an nan zamani zai iske wadansu jama’a da za su fita zuwa yakin zaukaka kalmar Allah, a rika cewa: shin ko akwai wanda ya taba zama da wanda ya yi abuta da Annabi (SAW)? Sai a ce, “Na’am, sai a ci nasara.” Zamani zai zo a rika cewa: Shin ko akwai wanda ya hadu da wanda ya hadu da sahabin Annabi (SAW)? A ce, “Na’am, sai a ci nasara.”               

Babi na Saba’in da Bakwai: Ba a kiran duk wanda ya mutu da sunan mai shahada. Abu Huraira (RA) ya ce, “Daga Annabi (SAW) cewa: “Allah Shi ne Mafi sani ga wanda yake jihadin daukaka kalmarSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga wanda aka yi masa rauni dominSa.”

583. An karbo daga kutaiba ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Suhail Sa’ad Sa’idi (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya hadu shi da mushirikai, sai suka yi yaki. Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya karkata da rundunarsa (kowa zuwa ga zangonsa). Saura (mushrikai) suka koma zuwa ga rundunarsa. A cikin sahaban Annabi (SAW) akwai wani mutum bai barin komai na kafiri face ya kashe ya kai sara da takobinsa. Sai (wani) ya ce: “Babu wanda ya kai jaruntar wane cikinmu a yau. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Amma kuwa lallai shi yana daga cikin mutanen wuta. Sai wani mutum daga cikin mutane ya ce: “Lallai ni zan zama mai lura halinsa har in gani yaya karshen rayuwarsa za ta kasance.” (mai ruwaya) Ya ce: “Sai ya fita tare da shi duk lokacin da (mutumin nan) ya tsaya sai ya tsaya tare da shi, idan ya yi sauri ya yi sauri tare da shi.” (mai ruwaya) ya ce: “Ana cikin haka sai aka yi wa mutumin nan rauni mai tsanani. Sai ya yi gaugawar ya mutu (ya huta), ya dora hannun takobinsa bisa kasa tsininsa a tsakanin kirjinsa. Sai ya hau bisa takobinsa ya kashe kansa. Sai mutumin da ke lura da sha’aninsa ya tafi ga Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘Na shaida lallai kai Manzon Allah ne. Ya ce: “Me ya faru? Ya ce, “Mutumin da ka ambaci halinsa dazu cewa: “Lallai shi yana daga cikin mutanen wuta, haka ya firgita mutane na ce, ni zan lura muku da shi, da na fita nemansa (bidarsa). Sai na iske an yi masa rauni mai tsanani, sai ya yi gaugawar mutuwa ya sanya kotar takobinsa bisa kasa tsinin yana bisa tsakanin kirjinsa. Sa’an nan ya hau bisa takobinsa ya kashe kansa.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, a wannan wuri: “Lallai mutum zai rika aiki irin aikin mutanen Aljanna bisa ga abin da  ke bayyana ga mutane alhali shi yana daga cikin mutanen wuta. Kuma za ku ga mutum yana aiki irin aikin mutanen wuta bisa ga abin da ke bayyana ga mutane alhali yana daga cikin mutanen Aljanna.”