Wata tanka dauke da litar man fetur dubu 45 ta yi hatsari sannan ta kama da wuta a yankin Egbeda na Jihar Legas.
Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) faruwar hadarin.
- Juyin mulki: MDD ta yi kira a saki shugabannin Mali
- Ya kamata matasa su rungumi noma ka’in da na’in – Shugaban NYSC
Ya ce da misalin karfe 12:20 na daren Talata hukumar ta samu labarin cewa tankar man ta kama da wuta a yankin Abule Ado cikin Karamar Hukumar Amuwo Odofin, lamarin da ya jefa mazauna cikin zullumi.
Ya ce NEMA da hadin gwiwar takwararta ta Jihar Legas sun bazama zuwa wajen da lamarin ya faru domin bayar da dauki da tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.
Sai dai ya ce: “Ba a samu hasarar rai ko barnar wata dukiya ko guda ba.”