Edita don Allah ka ba ni dama in yaba wa Shugaban Majalisar wakilai, wato Aminu Tambuwal dangane da matakin da ya dauka na fita daga PDP hakika shugaban ya yada kwallon mangwaro, ya huta da kuda, ganin yadda PDP ta zame wa ‘yan Najeriya karfen kafa. Don haka mu talakawa mun yi maraba da ficewarsa, tare da komawa APC. Fatan mu Allah ya kawo mana shugabanni masu adalci a Najeriya. Daga Aminu Abdu Baka noma Sani mainagge Kano 08099479880.
A maido mana da hijabin mu
Edita Lallai abin takaici ne da na samu labarin cewa Gwamna Fashola na Jihar Legas ya yi hani da sanya Hijabi a makarantu. Ko shakka babu wannan kokarin dakushe hasken addini ne. Domin kuwa addinin Musulunci da Kiristanci ya yi hani ga mata da su bude jikin su a bainar jama’a. Gwamna Fashola lawya ne. Sanin kanshi ne cewa sashe na hakkin bil Adama dake kundin tsarin mulkin kasar Najeriya ya ba da dama ga ’yan kasa da su gudanar da addininsu ba tare da tsangwama ba. Ina kira ga Gwamna Fashola da ya yi dubi da idon rahama da kuma janye wannan dokar ta hana sanya Hijabi Daga Comrade Abdulbaki Aliyu Jari katsina kofar kaura layout, Jihar katsina +2348035424321
Tur da miyagun matasa
Editan Aminiya, all’ummar Arewa maso Gabashin Najeriya muna Allah Wadai da wasu tsirarun matasa da ke kiran kansu matasan arewa har suke yunkurin tallafa wa Jonathan wajen sayen tikitin takarar shugabancin Najeriya, duk da irin ta’asar da aka yi mana a Yobe da Borno da Adamawa na rayuka da dukiyoyi, amma Jonathan ya kura ido ya kasa daukar matakin magance matsalar, sai ga wasu marasa sanin ya kamata na kokarin mayar mu gidan jiya. Allah Wadan naka ya lalace, kuma ina shaida wa wadannan matasa, su sani cewa ba Jonathan ba ko dan Arewa PDP ta tsayar ba za mu saurare shi ba. Daga Uthman bin Affan Malari Damturu. Jihar Yobe.
Matasa ba su saya wa Jonatahan fom ba
Edita a gaskiya muna nesanta kanmu da cewa kungiyoyin wasu matasa ne suka bawa Jonathan gudummawar kudi har Naira million 2 ya sayi form. Don haka nake sanar da al’ummar Jihar Kano da na kasa baki daya, a madadin ‘ya’yan kungiyar muryar talaka reshen Kano . da wasu da wasu gamayyar kungiyoyin matasan Jihar Kano. muna nesanta kammu game da wannan lamari. Idan kuka duba wajen da aka yi taron da suke fada cike yake da wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP. Sun yi wannan abu Daga anas Saminu Ja’en, kungiyar Muryar Talaka, Jihar Kano 07033882307.
2015: allurar cikin ruwa
Edita ga dukkan alamu wasu za su bukaci jin na ce allura ce a cikin ruwa, a harkar zaben kasar mu Najeriya. Ina da ’yan dalilai kamar haka tun bayan zaben shekarar1999, wanda jam’iyyu biyu ne suka fiddo ’yan takara na shugabancin kasa, wato PDP mai Cif Olushegun Obasanjo, da APP mai Cif Olu Falae, wanda a zaben 2003, da na 2007 zuwa na 2011, da wanda ke tafe na 2015, idan mai duka ya nufa mun kai, duka daga malaman zaben da jami’an tsaron da su kansu talakkawan da ’yan siyasar sai abin ya daure musu kai. Samun shugabancina kwarai na da sauki illa ni da ku mu cire son zuciya, mu kalli inda muka fito da inda za a nufa; mu yi abin da zai kawo wa al’ummar yau da ta gobe tarihi mai kyau a kasar Allah ya yi mana jagora a zaben shekara ta 2015. Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa.
Ga Gwamna Yari na Zamfara
Edita don Allah ku ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna A. A Yari, akan matsalar rashin biya wa ‘ya’yan talakkawa kudin jarabawar WAEC da NECO din da ba ta yi ba. Har yau, wanda shi ne ya hana a sako jsakamakon arabawar har yanzu. Kasancewar dole sai da wannan sakamakon ne ‘ya’yan talakawa za su samu zarafin wucewa makarantun gaba da sikandiren, domin zurfafa karatunsu.. Daga AbdulMalik Saidu Maibiredi, tashar Bagu Gusau.
Ga Shugabannin PDP
Edita, talakawan Najeriya ba da Izininmu ba, Shugabannin PDP suka tsayar da Shugaba Gudulok takara a 2015, domin ba za mu kara yarda mu kwanto wa kammu Kura ba, ta kara hallaka mu ba. Daga-Garba Nakwalo Ajaura Jihar Jigawa, 08060911100
Ta’aziyya ga asibitin Shehu Gidado
Editan Aminiya ka ba ni dama in mika sakon ta’aziyyata ga Hukumar Asibitin Shehu Gidado da ’yan uwa da abokan arziki a birnin Kano, game da rasuwar Likitansu, Dokta Isma’ila Ishaka Ya’u. Wannan marigayi ya kewaya asibitocin Gwarzo da dambatta, don haka su ma muna yi musu ta’aziyya. Allah Ya gafarta masa, Ya kuma kyauta namu karshen in ta zo. Amin. Summa amin. Daga Aliyu Umar 08065570493.
Yabo ga Jam’iyyar APC
Matakin da jam’iyyar adawa ta APC ta dauka, kan cewa ba ta da niyyar tsayar da mabiya addinai guda a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaba a zaben shekarar 2015, tana mai cewa za ta gauraya wadannan mukamai ne, tsakanin Musulmai da kiristoci, domin yin adalci da kuma tabbatar da fahimtar juna a tsakaninsu, to zahiri wannan wani abin a yaba ne kwarai, domin tunkarar warware matsalolin da ke ci gaba da addabarmu, da kuma tabbatar da ingantaccen zabe a fadin kasar mu baki daya. Daga Adam A. Adam Gashua 08189941495, 07037169739, 08024605583.
Sai Salihu Lukman a Kaduna
Editan Aminiya ka ba ni dama in nuna goyon bayan al’umma, musamman ’yan gwagwarmayar kwatar ’yancin talakawa, da mu hada kai mu tabbatar da Malam Salihu Lukman a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jagorancin Jam’iyyar APC. Muna fata kafofin yada labarai za su shirya muhawara a tsakanin ’yan takarar gwamna a Jihar Kaduna, ta yadda za a samar wa talakawa sauyi mai alfanu a cikin rayuwarsu. Don haka muna jiran Aminiya da gidajen rediyo da talabijin su aiwatar mana da wnanan managarcin aiki. Allah Ya ba mu Shugaba nagari wanda ke kishin gama-garin al’umma. Daga Dodo Rabi’u Yusif Kaduna
’Yan matan Chibok
Assalamu Alaikum Aminiya Ku ba ni dama in yi tsokaci akan ci gaba da tautaunawa da gwamnati ke yi da ’yan boko haram duk da haka kuma ana samun cigaba da hare-haren. Wannan shi ne gobara daga teku maganinki Allah a Kwana a tashi dai har an cika kwanaki 200, ke nan mata ’yan makarantar Chibok na hannun kungiyan yan boko haram. Gwamnati dai ta fara nuna gazawa. Don haka daukacin ’yan Najeriya mu hada karfi, mu bi duk hanyar da tadace don ceton kanmu. Allah Ya yi mana muwafaka. Amin. Daga Daga Ahmadu Manager Bauchi Anguwan Karofin Madaki.08065189242