Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga ci gaba da amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tambaya ta 27: Malama na ga kasidarki a jaridar Aminiya game da rabon kwana ga mai mata sama da daya, matata daya ba ta ba ni hakkina yadda ya kamata a duk ranar kwananta; ya ya zan yi da ita? Don Allah ki ba ni shawarar yadda zan yi a shari’ance.
-Muhammad
Amsa: Yadda za ka yi a shari’ance shi ne sai ka yi aiki da matakan ladabtar da mata mai bijirewa ga mijinta kamar yadda bayanin haka ya zo daga Allah Madaukakin Sarki a cikin aya ta 34 cikin Suratul Nisa’i:
“…Kuma wadanda kuke tsoron bijirewarsu to ku yi masu gargadi; (in sun ki) kuma ku kaurace masu a wuraren kwanciya; kuma ku doke su. Sa’annan kuma idan sun yi maku da’a, kada ku nemi wata hanya a kansu…”
Don haka matakan ladabtar da matar da take bijirewa ga mijinta, ko ba ta yin ladabi da biyayya a gare shi guda uku ne:
1. Gargadi: Maigida zai fara da yi mata nasiha mai shiga jiki cikin siga kyakkyawa, ya tunasar da ita girman Allah da alherin da ke cikin yi masa da’a, da kuma sakamako na azaba da kaskancin da zai sauka a kan duk wani mai bijirewa ga umarnin Allah Subhanahu Wa Ta’ala . Ya kafa mata misali da hadisan Manzon Allah da suka bayyana muhimmancin yin da’a ga miji, da girman azaba da kaskancin da ke tare da bijirewa ga miji a wajen kwanciya a cikin sauran huldodin rayuwar aure. Misali:
• Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya bayyana cewa duk macen da mijinta ya kira ta shimfidar barcinsu ta ki zuwa, mala’iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari.
• Haka kuma ya bayyana cewa duk matar da mijinta ya yi fushi da ita Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai yi fushi da ita har sai mijinta ya bar fushi da ita, kuma duk ibadunta ba za a karba ba har sai mijinta ya daina fushi da ita.
• Sannan a wani wurin kuma ya bayyana cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala da kanSa yana tabbatar da tsinuwarsa ga macen da idan mijinta ya kirawo ta don ibadar aure takan tsaya ta bata lokaci har sai barci ya kwashe mijin.
• Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umarni da cewa: “Idan miji ya kirawo matarsa (domin ibadar aure) ta je gare shi ko da tana bisa rakumi ne.” A wani wajen kuma “Ko da ta na gindin murhun girki ne.”
• Sannan uwar mu’uminai Aisha Allah ya yarda da ita ta yi kira ga matan wannan al’umma: “Ya ku mata! In da kun san girman hakkin da mazanku ke da shi a kanku, lallai da ko waccenku ta share dattin tafin kafar mijinta da fuskar ta!”
• Sannan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya tambayi wata Sahabiya Allah ya yarda da ita : “Ya kike da mijinki?” Ta amsa da cewa: “Ina iyakar kokarina gare shi sai dai a kan abubuwan da suka fi karfina.” Sai ya ce: “Ki kula sosai da yadda kike mu’amala da shi domin shi ne aljannarki kuma shi ne wutarki.”
• Haka kuma Annnabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce duk macen da ta mutu mijinta yana mai jin dadi da ita za ta shiga aljanna.
• Haka kuma ya ce duk macen da ta tsare sallolin farilla biyar, ta tsare farjinta, kuma ta yi da’a ga mijinta za ta shiga aljanna ta kofar da ta zaba.
To irin wadannan misalan ne maigida zai kwatanta wa Uwargidansa har Allah Ya sa zuciyarta ta narke, ta yi nadamar abubuwan da ta yi kuma ta tuba ta daina aikatasu. Amma in duk nasihohi da gargadi da jan kunnen da ya yi ba su hanata aikata aiyukan bijirewar da take yi ba sai a je ga mataki na biyu.
2. kauracewa: A wannan mataki maigida zai kauracewa matarsa a shimfidar aurensu, ya juya mata baya, ya ki kula ta ko nemanta da ibadar aure. Har sai ta ladabtu ta nemi gafara kuma ta yi nadamar abin da ta aikata sannan maigida ya janye wannan kauracewar. A kula da kyau cewa, a cikin daki, a shimfidar gado ne kadai ake kauracewa mace, amma a kaurace mata a cikin sauran bangarorin zamantakewar rayuwar aure; kuma kada a bayyanar da kauracewar nan har sauran jama’a su sani. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya fada cewa daga cikin hakkokin mace a kan mijinta shi ne kada ya kaurace mata sai a cikin gida kadai.
3. Bulala: Mataki na uku shi ne maigida zai hori da mata mai bijirewa ta hanyar duka, ko bugunta da bulala a jikinta. Shi bugun nan za a yi shi ne a dai-dai lokacin da take cikin bijirewa ga umarnin maigida, kuma za a yi shi ne sama-sama, watau kar ya cika zafi ta yadda har zai nuna alama a jikinta ko ya raunata mata fata, kuma matsakaici watau kar ya yi yawa ta yadda har zai sa ta kasa tashi ko ya kwantar da ita. Za a yi shi ne cikin irin yanayin yadda za a hori dan karamin yaron da ya yi laifi. Kuma a kula sosai kar a buge ta a saman fuska domin Manzon Allah ya yi hani da hakan; shi ya sa ya fi dacewa a sa bulala kar a yi dukan nan da hannu,bisa la’akari da karfi jikin da namiji da kuma rauni irin na jikin ‘ya mace.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.