✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko.…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tambaya Ta  5: Don Allah Duniyar Ma’aurata ku yi mana bayani a kan kwayar maganin nan na biagra, ita ma tana cikin kayan hakkin mayen da mata za su iya amfani da su? Don na ji an ce tana kara wa maza karfin sha’awa sosai. Ina son in sani ko yana yin aiki ga mata domin ni dai ina da matsalar sha’awa.
 — Hajiya daga Sokoto
Amsa: biagra ba kayan da’a ba ce, kuma ba kwayar karin karfin sha’awa ba ce, sannan maza ne kadai ke iya amfani da ita ban da mata, su ma din sai in ta kama ba haka kawai ba. A hakikanin gaskiya biagra asalinta magani ce da ake sha don neman waraka kamar yadda ake shan maganin zazzabi, dole sai Likita ya auna mutum, ya tabbatar yana da bukatar wannan magani, sannan a rubuta masa ita, amma kamar yadda ake wuce ka’ida wajen sha da yawa daga cikin magungunan nasara, to shi ma wannan magani da yawan mutane sukan wuce ka’ida wajen amfani da shi, sai ka ga lafiyayyen mutum yana sha ba bisa ka’ida ba.
biagra ta kasance ne a dalilin wani gam-da-katar da kamfanin da suka kirkire ta suka yi, a lokacin suna kokarin gwajin wani sinadari mai suna Sildenafil a wasu zababbun mutane, don ya zama maganin kasawa ko raunin zuciya, sai kawai suka lura da yanayin da sinadarin ke sanya mafi yawa daga cikin mutanen da ake amfani da su wajen gwajin, don haka sai suka watsar da binciken su na maganin kasawar zuciya, suka dukufa wajen inganta sinadarin don ya zama maganin matsalar sanyin gaba na maza. biagra sunan kasuwa ne da aka sa ma wannan sinadarin na Sildenafil a matsayin maganin sanyin gaba ko kasawar mazakuta ta maza. Don haka mata ba su yin amfani da biagra, sai dai nan gaba wata kila a sarrafo wacce za ta yi amfani ga gyara lafiyar sha’awar mata.
Tambaya Ta 6: Don Allah ku yi mana bayanin yadda biagra ke aiki wajen kara karfi sha’awa, domin ina son in fara amfani da ita don magance sanyin sha’awar da ke damuna.
Daga Musa dan Dattijo Funtuwa.
Amsa: Don fahimtar yadda biagra ke aiki, ga bayani a kan halittar al’aurar namiji da kuma yanayin kasantuwar sha’awars: Al’aurar da namiji tana dauke da wasu jijiyoyi masu raga-raga guda uku da suka ratsa ta cikinta, jijiyar da ke fitar ta fitsari ta ratsa daya daga cikin wadannan jijiyoyin. Saboda yanayin halittarsu, mai kamar yadi-yadi (ko soso-soso), suna saurin tsotsar jini kamar yadda soson katifa kan tsotso ruwa lokacin da a ka saka shi cikin ruwan.
Har sai wadannan jijiyoyi sun kumbura taf da jini ne sannan namiji ke iya kasancewa cikin yanayin gabatar da ibadar aure. Wasu jijiyoyin watsa jini guda biyu ne ke isar da jini ga wadannan jijiyoyin, duk lokacin da wadannan jijiyoyi suka samu matsala, kamar idan hanyar jinin ta toshe a dalilin rashin isasshiyar iska ko kitsen da ke yawo cikin jini ya yi yawa har ya toshe hanyar jinin, da sauran wasu matsalolin da yawancin ciwuka masu nasaba da zuciya: irinsu kasawar zuciya, hawan jini, matsananciyar kiba da ciwon siga ke haifarwa, to hakan na iya haifar da matsalar kasawar mazakuta ga maza.
Wasu ’yan kananan jijiyoyi da ke rarratse cikin wadancan manyan jijiyoyin guda uku ke kula da gudanarwar jini a cikin wannan halitta, idan manyan jijiyoyin sun kumbura da jini, sai su kananan su mimmike, ta yadda za su zama kamar wani murfi da zai rufe hanyar da jini zai bi ya fita, har sai lokacin da aka cim ma biyan bukatar ibadar ne, sannan za su kwanta sai jinin ya kwarare ya fita. Wasu cututtuka da magungunan wasu cutakan (misali: na hawan jini da ciwon siga), tsufa ko yawan damuwa, na iya sa kananan jijiyoyin nan su kasa mimmikewa, don haka kofar fitar jini sai ta kasance rabi a bude ko ma a bude gaba daya, don haka jinin ba zai tsaya ba balle har a samu kasancewa cikin yanayin aiwatar da ibadar aure.
Komai da ke faruwa cikin jikin mu za ka tarar akwai wani sinadari ko wasu sinadarai wadanda idan babu su, ko idan sun samu matsala, faruwar wannan al’amari ba zai yiwu ba, to haka ma al’amarin ibadar aure, tun da farkonsa har zuwa kammaluwarsa, akwai sinadarai daban daban, hawa-hawa da za su yi ta zirga-zirga cikin jini, suna kai kawo don tabbatuwar wannan gagarumin aiki da ya kunshi kusan dukkan illahirin gangar jikin dan Adam. Daga cikin irin wadannan sinadaran, akwai wadanda ake sakewa cikin jini musamman domin sanya kananan jijiyoyin nan kwantawa har jini ya samu kwarara cikin wannan halittar.
biagra na aiki ne wajen tsayar da sinadarin karshe da ke aikin malalar da jini cikin al’aura yayin aikatuwar ibadar aure, ta yadda ba zai daina aiki ba har tsawon wani lokaci, domin tana like sinadarin da a kan turo don ya tsayar da wancan sinadarin daga aiki, ta hana shi aiwatar da aikinsa, wanda ba don haka ba, da ya tsayar da sinadarin da ke aikin malalar da tsayawar jinin cikin al’aura ya zama da wahala, domin sai jinin ya kwarare ya fita, halittar sai ta koma a yadda take a da.
Don haka, biagra ko kusa da zama abin karin kuzarin sha’awa ba ta yi ba, hasalima, idan ba ka jin motsuwar sha’awa, ko kana da karancin sinadarin sha’awa, to biagra ba za ta iya yin komai ba ta wannan bangaren ba, shi ya sa a ka’ida ta kimiyya, dole sai likita ya auna ya ga cewa ba wai matsalar karancin sha’awa ko toshewar hanyoyin jini ko tsananin huzni ne ke damun marar lafiya kafin a ba shi damar amfani da biagra ba. Don haka masu shan biagra ba bisa ka’ida ba, musamman masu sha don su yi ta zinace-zinace da sauransu, suna ganin hakan isa ce da kai wa kololuwa wajen wayewa da birnancewa, to su sani suna jefa rayuwarsu cikin hadari ne kawai.