✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 13

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.

Tambaya ta 29: Na yi aure yanzu tsawon wata uku amma mijina bai taba ba ni hakkina na aure ba, na rasa yanda zan yi, shi ne nake neman taimako ki ban kyakkyawar shawari, in fada a gida ne ko ya ya zan yi?
Amsa: Abu na farko mafi dacewa da za ki yi shi ne hakuri; ki sani, duk wanda ya yi aure, ana kyautata zatton ya yi shi ne don raya SUNNAR Annabi sallalahu alaihi wasallam da kuma fatan samun zuriyya dayyaba; don haka duk wani sabon angon da ya aikata kwatankwacin abin da angonki ya yi, lallai yana da wani babban dalilin da ya sa shi aikata hakan; kamar yadda Hausawa kan ce abin da ya kori bera cikin wuta, lallai ya fi wutar zafi. Abu na biyu mafi dacewa kuma sai ki tuntube shi ta hanya mafi dacewa kuma cikin nuna ladabi da kulawa; kar ki tuntube shi cikin  haushi da nuna zargi domin yin haka na iya kara dagula al’amarin. In an dace ya ba ki fuska kun tattauna game da matsalar, to shi ke nan, sai ku hada kai ku yi kokarin magance ta. In yana da wata matsala ne dangane da sha’awa, sai ki ba shi kwakkwaran goyon bayan samun maganin matsalar. Idan kuma akwai wani abu daban da ya hana shi gabatar da ibadar aure, sai ki nemi hanya mafi dacewa ta warware wannan matsalar. In kuma ya ki ba ki fuska ku tattauna; ki dai ci gaba da hakuri, kuma ki ci gaba da kyautata masa da nuna kulawa cikin sigar so da kauna da sha’awa. Ki rika yawan jansa da hira cikin zaurance irin na so da kauna, da yin wasanni masu tokuno sha’awa, da dai duk sauran abubuwan da kika fahimci za su taimaka ta wannan fannin. Sannan ki yi kokarin wanzar da kyakkyawan aminci a tsakaninku ta yadda a hankali zai ji saukin sanar da ke dalilin da ya sa har yanzu bai kaddamar da daren farkon aurenku ba. Wata kila tsananin kunya da fargaba ne suka sa hakan bai faru ba, shimfida kyakkyawar amintaka zai kawar da su ire-iren wadannan, ya kuma rayar da ibadar aure a tsakaninku. Amma idan bayan duk kin aikata wadannan ba ki ga canjin da kike fatan samu ba daga angon naki, to sai ki fara da gargadin sa cewa ke fa  za ki je ga magabatanku don a sama maku mafita tun da shi dai ya ki baki hadin kai. In wannan ta sa ya farga ya yi abin da ya dace, shi ke nan. In kuma bai yi ba, to sai ki sanar da magabatanki don a bincike shi a ji abin da ya sa ya aikata haka. Ina yi maki addu’ar Allah Ya daidaita dukkan al’amura tsakaninki da angonki, amin.
Tambaya ta 30: Don Allah ki yi mana sharhi a kan masu kishi da makwabtansu, sannan mene ne matsayin gasa a babin kishi, komai wani ya yi ka ce sai ka yi ko ka yi wanda ya fi shi?
-Amina Maman Faruk, Faskari Close S/gari Kaduna.
Amsa: Kishi da makwabta, in har an yi shi ne a kan abin da ya dace, kuma a cikin yanayin da ya dace, to wannan babu laifi. Kamar misali wata mace ta ga yadda makwabciyarta take da tsabta da iya kula da gida, ita ma ta dage da yin haka. Ko maigida ya ga yadda makwabcinsa yake  dagewa wajen kula da tarbiyar iyalansa shi ma ya yi koyi da haka. Amma idan za a yi haka ne don takama da nuna isa da bajinta don burge wasu jama’a kawai to wannan bai halatta musulmin kirki ya yi irinsa ba. Kishi mai kyau kala biyu ne: Na farko shi ne kishi na lahira wanda yake abin so ne ga dukkan musulmi ya kasance ya mallaki isasshen kishin ghira cikin zuciyarsa. Ghira shi ne jin haushi, bacin rai da kyama da sukan bayyana a cikin zuciyar namiji ko mace dangane da kusantuwar wani nasu, kamar miji, mata, ’ya, mahaifa tare da wani wanda ba nasu ba. Kamar duk lokacin da miji ya ga matarsa tare da wani mutum wanda ba muharraminta ba, sai ya ji yana kishin abin ko da kuwa a halartaccen yanayi ne, ko miji ya ji yana kishin bayyanar adon matarsa ga wasu mazan da ba muharramanta ba. Kishin ghira shi ke sa maza su rika dagewa wajen  tsare matansu da ’ya’yansu daga bayyanar adonsu da kwalliyarsu ga mazan da ba muharramansu ba. Kishin ghira kuma shi ke sa mata su rika jin ba su son kusantowar mazan su da wasu matan in ba su ba, kuma shi ke sa su jin haushin kishiyoyinsu da yin rige-rigen faranta zuciyar maigidansu.
Kishi na biyu mai kyau shi ne kishi domin Allah; watau ka ga wani bawan Allah ya dage ya yi wani abin kirki kai ma ka ji kana son ka yi wannan abin kirkin, ko ka ji kana son ka wuce inda wani ya kai ga kyakkyawan hali ko kyautata ibada. Kamar maigidan da yake kishin iyalinsa ta yadda hakan yake sa wa ya dage ya ga ya samar masu dukkan kayan bukatun rayuwa.Ko kishiyoyi biyu da suke rige-rigen nuna kulawa da kyautatawa ga maigidansu, kowace ba ta son a bar ta a baya. Amma kishi mai kunshe da hassada, tsana da son ta kowane hali sai an zarce abokin hamayya, to wannan  za a kira shi ne mummuna kuma bakin kishi.
Matsayin gasa a babin kishi ya halatta musamman a tsakanin kishiyoyin juna guda, ta yadda za su rika rige-rigen faranta ran maigidansu, sannan a babin addini ma ya halatta in dai da kyakkywar niyya domin Allah za a yi gasar ba da nufin nuna isa da girman kai ba, ko don a nuna ai ni wane bai isa ya ce ya fi ni ba balle ma har ya wuce ni.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.