✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayi Google

Tambayi Google Wata rana wani Bahadeje ya sayi sabuwar waya (Android), sai ya nuna wa abokinsa. Abokin nasa ya karba ya gani, sai ya fara…

Tambayi Google

Wata rana wani Bahadeje ya sayi sabuwar waya (Android), sai ya nuna wa abokinsa. Abokin nasa ya karba ya gani, sai ya fara shiga yanar gizo. Bahadeje ya ce: “Me kake yi ne?” Ya ce masa ai ya shiga Google ne. Ya tambaya: “Mene ne kuma Google?” Abokin ya ce masa ai shi Google wani wuri ne da duk abin da kake nema idan ka rubuta tambaya za su rubuto maka amsa har su nuna maka Bidiyo. Ya gwada masa kuma ya gani. Bayan kwana biyu sai ga Bahadeje ya dawo wurin abokinsa, ya mika masa wayar, ya ce: “Yau Google zai yi mini amfani. kanwata ce mijinta ya yi mata duka har ya fasa mata jiki. Don haka ka shiga Google ka tambaye su, Me ta yi wa mijinta ya yi mata duka? Haka kuma idan da hali har Bidiyo nake son su nuna mini, don na samu hujja, domin in san irin matakin da zan dauka.”
Daga Mudassir Maishayi Ningi, 08169139393
 
Cigiyar kudi

Wani Bakatsine ne ya zubar da kudi sai ya zo yana ’yan dube-dube bai dai yi cigiya ba. Wani Bahadeje ya gan shi sai ya ce masa: “Malam, hala cigiya kake ko?” Ya ce masa: “kwarai kuwa.” Ya kara tambaya: “Shin kudi ne ko?” Ya ce: “kwarai kuwa.” Bahadeje ya ce: “Yan dubu-dubu ne ko?” Ya ce: “kwarai kuwa.” Ya kara tambaya: “daure suke da tsumma cikin leda ko?” Bakatsine ya ce: “kwarai kuwa, su ne, kudina ne.” Jin haka sai Bahadeje ya ce: “Gaskiya ban gansu ba!” Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933

Soyayyar Bagobiri

Wani Bagobiri ne ya ji mai wa’azi yana cewa: “Ku kasance masu yawan yaba wa matanku yayin da suka yi maku abu, musamman idan suka yi girki, ku rika yin santi gami da yaba masu cewa ya yi dadi. Hakan zai kara wa zamantakewarku armashi.” Ko da Bagobiri ya koma gida, yana cin abinci sai ya dubi matarsa ya ce: “Tun da uwata ta haife ni ban taba cin abinci mai dadin wannan ba. Fadin hakan ke da wuya matar ta tashi a fusace ta juye masa sauran miyar a ka, ta ce: “Yau shekararmu 20 da kai, ba ka taba yabon abincina ba sai yau da na taho da shi daga gidan biki? Daga Sadik Hadeja, 08134860283

Lokacin hunturu

Wata gyatuma ce tana zaune a daki sai ta ga ’yarta tana amai, amma ba ta fita ba balle ta tambaye ta abin da ke faruwa, domin ta dade da sanin cewa ciki ne ’yar tata take dauke da shi. Da safiya ta yi sai ta je dakinta, ta tarar da ita tana kwance. Bayan sun gaisa sai uwar ta ce: “Kai irin wannan sanyin hunturu haka, ai shi ke sa a dau ciki.” Nan da nan sai diyar ta ce: “Haka kuma fa mama, ina ganin shi ya sa na dau ciki!”
Daga Safiyat Usman, 09031513811