✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya

Wani malamin makaranta ne yana koyar da darasin tarihi a aji, sai ya tambayi dalibai cewa: “Waye ya kashe Abu Jahil?” Sai wani yaro ya…

Wani malamin makaranta ne yana koyar da darasin tarihi a aji, sai ya tambayi dalibai cewa: “Waye ya kashe Abu Jahil?” Sai wani yaro ya daga hannu ya ce: “Wallahi ba ni na kashe shi ba, kuma ban san wadda ya kashe shi ba.” Malamin ransa ya baci, ya kirawo shugaban makarantar zuwa ajin. Bayan sun zo shugaban ya maimaita tambayar da malami ya yi masu a baya. Yaron ya sake tashi ya maimata abin da ya fada a baya. Jin haka sai shugaban ya ce wa malamin: “Wai don Allah a ajin nan aka kashe Abu Jahil din?”

Isah Ramin Hudu, Hadeja, 08060353382