Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana dakatar da yunkurin Gwamnatin tarayya na janye tallafin man fetur a matsayin abun farin ciki ga ’yan Najeriya.
Da yake zanta wa da menam labarai, Shugaban kungiyar Reshen Jihar Kano, Kabiru Ado Minjibir, ya ce abun a yi murna ne saboda cire tallafin zai haifar da karin tsadar man fetur wanda hakan zai jefa miliyoyin mutane cikin tsaka mai wuya.
- Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci
- Harin IS ya raba mutum dubu 45 da muhallansu a Syria
Minjibir, ya yi wannan jawabi ne yayin da yake yi wa mambobin kungiyar bayani dangane da yadda gwamnati ta yi mi’ara koma baya game da janye kudurin karin kudin mai.
Aminiya ta rawaito yadda Kungiyar Kwadago ta Najeriya Reshen Jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar ’yan kasuwa suka shirya shiga babbar zanga-zangar da aka shirya yi wa Gwamnatin Tarayya kan batun karin kudin man fetur.
Kungiyoyin sun shirya sanya kafar wando daya da gwamnatin ne a kan shirinta na kara kudin man fetur da kuma janye tallafi a kansa, wanda aka dade ana tirka-tirka a kai.