✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talata za a fara gasar Zakarun Kulob na Turai

A ranar Talata 12 da kuma Laraba 13 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka…

A ranar Talata 12 da kuma Laraba 13 ga watan nan da muke ciki ne za a fara gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da (Champions League).

kungiyoyin kwallon kafa 32 ne za su fafata a tsakaninsu don a samu zakara.

Wasannin dai za su gudana ne a mataki-mataki.  An karkasa kungiyoyi ne zuwa rukuni takwas, inda kowane rukuni yake kunshe da kungiyoyi hurhudu da za su fafata a tsakaninsu.  kungiyoyi biyun da suka kasance a saman teburin kowane rukuni ne za su haye zuwa matakin zagaye na biyu daga nan a sake zubar da kungiyoyi 8 don a yi wasan kwata-fainai, daga nan a zubar da hudu don a yi wasan kusa da na karshe, semi fainal daga nan kungiyoyi biyun da suka samu nasara ne za su buga wasan karshe, fainal.

Kulob din Real Madrid na Sifen ne ke rike da kofin, kuma a jumulla ita ce ta taba lashe kofin sau 12 a tarihin gasar.

Daga cikin kungiyoyin da za su yi wasa a ranar Talata mai zuwa suna hada da Manchester United da Chelsea daga Ingila sai FC Barcelona da Atletico Madrid daga Sifen.  Bayern Munich ta Jamus ma tana da wasa a ranar.

A ranar Laraba kuwa, kungiyoyin Real Madrid da na Liberpool da Tottenham da Manchester City duk suna da wasa a ranar.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil inda daruruwan ’yan kallo za su halarta don ganin yadda wasannin za su kaya.

Za a yi wasan karshe ne a birnin Kieb na Ukraine a ranar 26 ga watan Mayun 2018.