✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talata za a fara gasar Kofin Zakarun Kulob na Turai

A ranar Talata mai zuwa ne idan Allah Ya kai mu ake sa ran za a fara fafatawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da…

A ranar Talata mai zuwa ne idan Allah Ya kai mu ake sa ran za a fara fafatawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da wato UEFA Champions League.
Kimanin kungiyoyin kwallon kafa daga sassan Nahiyar Turai 32 ne za su fafata a matakin farko inda 16 za su haye zuwa zagaye na biyu daga nan a sake zaftare takwas don bugawa a matakin kwata-fainal daga nan sai hudu da za su buga wasan kusa-da karshe kafin a samu biyu da za su buga wasan karshe, inda za a samu kungiyar da za ta lashe kofin.
Kulob din Real Madrid daga kasar Sifen ne ya lashe kofin a bara, bayan ya doke na Atletico Madrid shi ma daga Sifen a bugun daga finareti a wasan karshe. Kulob din na Real Madrid ne ya fi kowane kulob yawan lashe kofin a tarihin gasar, inda ya samu nasarar lashe kofin sau 11.  
Sai kulob din AC Milan na Italiya ke biye da shi bayan ya lashe sau 7.   Sai kulob din Liberpool na Ingila da FC Barcelona na Sifen da kuma FC Bayern Munich na Jamus da suka lashe kofin sau biyar-biyar.
Kulob din Manchester United ya taba lashe kofin sau uku, yayin da kulob din Chelsea ya lashe sau daya. Kulob din Arsenal da Manchester City da ke Ingila da PSG na Faransa da Atletico Madrid na Sifen ba su taba lashe wannan kofi ba.
Ga jadawalin yadda za a buga wasannin na ranar Talata da kuma Laraba mai zuwa kamar haka: