A ranar Lahadi ne al’ummar Jihar Kano suka wayi gari da fastocin takarar shugaban kasa na Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.
Wannan ya kara adadin fastocin masu neman takarar shugabancin kasar da suka bayyana a kwaryar birnin Dabo.
Daga cikin wuraren da aka manna fastocin takarar gwamnan na Bauchi sun hada da titin Zariya, Gadar Lado, titin Gidan Zoo, shataletalen Dangi da kuma wasu wuraren a fadin jihar.
Ana iya tunawa cewa, fastocin ’yan takarar shugabancin kasa da suka hada Bola Tinubu, Atiku Abubakar na daga cikin wanda suka kwana biyu da karade kafatanin birnin Kano.
Fastocin da wasu matasa masu ikirarin kishin kasa da ke goyon bayan Gwamna Bala Mohammed a zaben 2023, na dauke da rubutun: “Don ciyar da Najeriya gaba a 2023.”
A makon da ya gabaya ne Gwamnan ya bukaci a bashi makonni uku ya nemi shawarwari dangane da bukatar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin da wata kungiyar Matasan Arewa ta Northern Youth Leaders Forum (NYLF) ta gabatar masa da wasikar neman ya bayyana bukatar tsayawa takarar a babban zaben da ke tafe.