Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da zabar duk wani dan takara da bai hada tafiyarsa da ta Kirista da Musulmi ba a zaben 2023.
Lawal ya ce, akwai bukatar bijire wa takarar APC ta Musulmi biyu a zaben 2023.
- Rashin ofishin jakadanci na ci mana tuwo a kwarya – ’Yan Najeriya mazauna Bangladesh
- An kama tirela 2 makare da katan 2,000 na giya a Kano
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zabi Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, wanda shi ma musulmi ne, a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya harzuka masu ruwa da tsaki, musamman ma Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Da yake tsokaci kan haka a taron shugabannin Kiristocin Arewa na jam’iyyar APC a Abuja, Lawal ya yi ikirarin cewa akwai wata manufa ta son murkushe Kiristocin Arewa.
“Za mu kare kanmu. Za mu yi amfani da katin zabe da kuma addu’o’i a zaben 2023.
“Takarar Musulmi da Musulmi na APC wani shiryayyen abu ne da aka kulla. Don haka, duk wanda ya yi maganar cancanta a matsayin dalilin zaben mataimaki musulmi, ya fadi son ransa ne. Wannan shiri ne nuna wariya ga Kiristoci.
“Wani zai iya tambaya; me ya sa ita kanta jam’iyyar APC ta yi shiru game da kin amincewarmu da takarar musulmi da musulmi? Kuma me ya sa babu wanda ya nemi Kiristoci don tattaunawa?
“Me ya sa a maimakon hakan sai suka dauki hayar limaman coci na bogi wajen kaddamar da abokin takarar Tinubu? Me ya sa suke son yakar CAN a kafafen yada labarai maimakon neman a yi sulhu? Hakika, gaskiya na fitowa.
“Muna kallon wannan takarar a matsayin nuna wariya ga Kiristocin Arewacin Najeriya ta fannin ilimi, tattalin arziki da siyasa.
“Wannan yanayin shi ne abin da muka samu dukkan hukumomin gwamnatocin arewa. Don haka, muna kallon wannan takarar ta musulmi biyu a matsayin wani abu na daban wanda ya saba wa ka’ida.