✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takarar Kano ta Tsakiya: Rufa’i Hanga ya maye gurbin Shekarau a NNPP

Bayan ficewar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam'iyar NNPP, Malam Ibrahim Shekarau, jam'iyar ta maye guirbinsa da Sanata Rufa'i Sani Hanga

Bayan ficewar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyar NNPP, Malam Ibrahim Shekarau, jam’iyar ta maye guirbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga.

Shekarau dai ya bar jam’iyar ta NNPP ne zuwa PDP, a kwanakin baya, wanda hakan ya tilasta wa jam’iyar neman wanda zai yi mata zawarcin kujerar a zaben 2023.

An dai tabbatar da takarar Sani Hangan ne a filin taro na Sani Abacha Youth Center da ke Kano ranar Alhamis, karkashin jagorancin shugaban jam’iyar na mazabar ta Kano ta Tsakiya, Abdullahi Zubair, kuma daruruwan magoya bayan jam’iyar daga kanana hukumomi 15 na mazabar sun halarta.

Tun bayan ficewar Shekarau daga NNPP din magoya bayanta ke ta bayyana ra’ayoyinsu kan wadanda suke ganin sun fi cancanta da zawarcin kujerar daga ciki da wajen jam’iyar.