A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020, Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai, ya nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 a tarihin masarautar.
Ambasada Bamalli ya zama sarki na farko daga gidan Sarautar Mallawa tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Alu Dan Sidi, shekaru 100 da suka gabata.
- Sabon Sarkin Zazzau ya shiga fada
- Ahmed Bamalli ya zama Sarkin Zazzau na 19
- Jana’izar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris (1936-2020)
Nadinsa a matsayin sarkin Zazzau na 19 ya biyo bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris, Sarki na 18 wanda ya mutu a ranar Lahadi, 20 ga Satumbar 2020 bayan ya yi shekaru 45 yana mulki.
Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau, rawanin da mahaifinsa marigayi Nuhu Bamalli ya daura yayin da kakansa, Dan Sidi, shi ne sarkin Zazzau na 13, wanda ya yi sarauta tsakanin 1903 da 1920.
Kafin nadinsa, shi ne Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Thialand da kuma Myannmar.
Ya kasance Kwamishina na Dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna a shekarar 2015.
Ya yi aikin Banki har ya kai mukamin Babban Darakta sannan daga baya ya zama mukaddashin Manajan-Darakta a Hukumar Buga Takardun Kudi ta Najeriya.
Tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Birane ta Abuja kafin ya zama shugaban masu kula da ma’aikata a MTel, sashen sadarwa na tsohon Kamfanin Sadarwa na Nijeriya (NITEL).
Bamalli wanda aka haifa a ranar 8 ga Yuni 1966, ya yi karatun Lauya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sannan ya yi digiri na biyu a kan alakar kasa da kasa da diflomasiyya da kuma difloma kan jagoranci a Jami’ar Oxford.