✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taimakon al’umma ya fi tafiya Umra a Ramadan – Liman Bunza

Limamin masallacin Juma’a na tsohowar kasuwa Bunza da ke Jihar Kebbi shehin Malami Imam Hali Bunza, ya bayyana cewa masu hannu da shuni da suke…

Limamin masallacin Juma’a na tsohowar kasuwa Bunza da ke Jihar Kebbi shehin Malami Imam Hali Bunza, ya bayyana cewa masu hannu da shuni da suke rige-rigen zuwa aikin Umara a cikin watan Ramadan su taimaka wa talakawa ya fi zuwa Umara lada.

Shehin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu na jim kadan bayan ya gama tafsir a masallacin juma’a na tsohuwar kasuwa a garin Bunza.  Imam Hali ya ce a addinin musulunci mutum ya taimaka wa talakawa marasa karfi da abinci da sutura da wurin zama da ba su jari, sannan ya tafi aikin umarar shi ne ya fi lada maimakon ya tafi aikin umarar ba tare da ya yi wadannan abubuwa ba.

Ya ce umara a rayuwa baki daya sunnah ce mutum ya yi ta sau daya, amma idan ya samu dama zai iya maimatawa. Idan mutum ya yi umara sau daya to ya tsaya ya taimakawa marasa karfi da abinci da sutura da wurin zama da yin karatu ya fi lada, da mutum ya yi ta maimata zuwa aikin umara. Amma umara tana nan da darajarta da ladanta musamman a lokacin azumin Ramadan.

Sheikh Hali ya ce idan Musulmi ba shi da abinci da sutura da wurin zama yana da hakki a kan sauran ’yan uwa musulmi su taimaka masa domin bai halatta musulmi su bar ’yan uwansu da yunwa su kuma suna cikin koshi ba. Ya ce a saya wa mutum gidan da zai zauna tare da iyalinsa da abinci da sutura ya fi lada a kan damar tafiya aikin umara.

Iman Hali ya ce idan mutum yana da hali to ya je ya yi  umararsa, amma maimakon ya debi mutum 10, ya biya musa umara gara ya sauke wa mutum 3 daga cikinsu matsalolin rashin gida da abinci da karancin jari, yin haka ya fi lada maimakon biya musu kudin zuwa umara, saboda tallafawa jama’a wajen samun abinci da sutura da wurin zama ceton rai ne, don haka ne ma Allah Madaukakin Sarki Ya yi ta nanata a taimaki misikinai da fakirai a cikin  Ayoyin Alkur’ani Mai Girma, sannan Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar da ciyar da mabukata saboda haka tausaya wa na kasa ya fi zama wajibi, domin mutum ya yi abin da al’umma za ta amfana ya fi ya yi abin da shi kadai ne zai amfana.