An saba da jin labarin tagwaye da yadda suke yin nasara a wasu harkoki, sai dai wannan labarin na tagwayen farfesoshi; Hassan da Hussaini ya zo da wani sabon salo da ba a saba gani ba a Nijeriya.
Tagwayen, masu kama da juna da suka taso a garin Kaduna sun kasance suna aiwatar da komai nasu iri daya tun tasowarsu suna kanana har zuwa zamowarsu farfesoshi.
Sun kasance a tare a dukkan lamuransu ba tare da barin wani abu ya raba su ba har zuwa yau.
A wurin wadannan ’yan biyu, rayuwa cike take da kalubale da fadi-tashi, sai dai hanyar shawo kan matsalolin rayuwar suke samar da sauki a cikinta.
A halin yanzu dai Hassan da Husain farfesoshi ne a fannin Harkar Noma inda suka kammala diigirin digirgir dinsu a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
Sun yi karatun digirinsu na farko ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Kafin nan, tagwayen sun yi karatunsu na firamare a tare ne har zuwa shigarsu jami’a kuma komai iri daya suke yi, sun yi aure a rana guda kuma dukkansu suna da ’ya’ya biyar-biyar, kowane na da maza huɗu da mace ɗaya.
Wani abin ban-sha’awa har ila yau game da wadannan tagwaye, shi ne yadda suka zabi karantarwa dukkansu a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina.
“Mun yi amanna cewa babban hanyar da za mu taimaka wa al’umma don ta samu ci gaba shi ne taimaka mata ta fannin ilimantarwa, wannan ya sa muka zabi koyarwa don samar da kasa tagari,” in ji Husaini.
“Duk da kasancewar Hassan da Hussain mutane masu shiru-shiru, amma hakan bai hana su aikin koyarwa ba duk da irin wahalar da ke tattare da hakan.
“Dukkanmu mun rike mukamai daban-daban da suka hada da shugaban sashen jarrabawa da mataimakan darakta da daraktoci da shugabannin sassa da sauran mukamai a wannan jami’a, tun kafin mu kama koyarwa gadan-gadan, wanda wannan zai nuna maka cewa komai namu a tare yake tafiya,” in ji shi.
Wasu da yawa sun ɗauka a rana ɗaya suka fara aiki a Jami’ar FUDMA, sai ba haka lamarin yake ba, domin sun bayyana cewa a rana ɗaya suka je intabiyu amma Hassan ya riga samun aiki inda ya fara a shekarar 2013 yayin da shekara ɗaya bayan nan a 2014 shi ma Hussaini ya kama aiki a wurin.
Sai dai duk da haka, sun sun fara gabatar da lacca ce tare a ranar 6 ga watan Fabrairun 2024 a Sashen Tattalin Noma (Agricultural Economics), sashen da suke aiki a jami’ar.
Kamanninsu ta kai ga yadda da wuya ka iya bambance su sai dai a duk lokacin da dalibai suka tunkari daya daga ciki don warware musu wata matsala, duk wanda aka tunkara yakan karbi damuwar ya magance musu ita ko da ya san ba tasa ba ce.
Wata daliba da ke mataki na 500 a fannin Tattalin Noman, a jami’ar mai suna Suwaibat Abdulmalik ta ce, “Abin na da matukar burgewa domin idan Hassan ya bayar da aiki a wani lokaci mukan kai wa Hussain ne, haka idan Hussaini ne ya bayar da aikin sai mu kai wa Hassan idan mun gama kuma haka kowa zai karba ba tare da ya ce ba nasa ba ne mu je wajen dayan ba.”
“Hakan ya taimaka matuka musamman wajen bayar da wahalar tantance wane ne ba wane ne ba a tsakaninsu.
“Duk wanda ka samu a ciki kamar ka samu dayan ne ba tare da sun nuna maka cewa ba wurin dayan ba, wurin dayan za ka saboda suna da matukar kama.”
Wani abin da ke wahalarwa wajen bambance tsakaninsu shi ne yanayin shigarsu da sanya tufafinsu domin a mafi yawan lokuta sukan sa kaya iri guda ne.
A irin wannan lokaci, kamar yadda Suwaiba ta ce, idan ma mutum ya gansu a tare a lokaci guda ba kowa ne zai banbance wane ne Hassan kuma wane ne Hussaini a cikinsu ba.
Ta ce a haka dalibai ke hulda da su kuma su ma haka suke hulda da dalibai saboda sun san kansu, in ji Suwaiba Abdulmalik.
Shi kuwa wani dalibi mai suna Muhammad Malle Abubakar wanda ya kammala digirinsa na farko kuma yanzu haka yake digiri na biyu a wannan sashe, ya ce dadewar da ya yi tare da su bai taimaka masa da komai ba wajen banbance su.
Muhammad Malle ya ce, “Tagwayen suna da matukar kama ta yadda babu wani a wannan sashe, dalibi ne shi ko malami da zai iya bambance maka su cikin sauki ya ce maka wane shi ne Hassan, wane shi ne Hussaini, kai kamanceceniyarsu a komai ne hatta a halaye da dabi’u da ayayyakunsu abin ya fi karfin tunanin mutum,” in ji shi.
A gida kuwa, wadannan tagwaye sun kasance aminan juna, baya ga kasancewarsu ’yan uwa wadanda suke matukar kaunar junansu.
A rana guda aka daura musu aure kuma a lokaci guda amma duk da haka sai da kowane ya halarci bikin dan uwansa da aka gudanar a watan Nuwamban 2006.
Allah Ya azurta su dukka da samun ’ya’ya biyar-biyar kowa na da maza hudu da mace daya kuma kansu a hade yake su goman.
Matansu da suka fito daga wurare daban-daban sun hada kansu wuri daya kan abin da mazansu ke so kuma suna aiki tukuru su ma don taimaka wa iyalan wajen ci gaba da alakar da suka tarar da su a kai.
Duk da cewa ba a wuri daya suke zama a cikin kwaryar Katsina ba, amma iyalansu kan ziyarci juna a-kai-a-kai a kowane irin lokaci dare ko rana.
Hatta ’ya’yansu suna shan matukar wuya wajen bambance maihaifansu, domin kowane yakan yi wa kowanensu abin da mahaifi kan yi wa ’ya’yan cikinsa.
Yaran na ganin iyayensu a tare a kowane lokaci kuma suna daukar dawainiyarsu ba tare da nuna bambamci ba.
Khalid, babban dan Farfesa Hussaini ya ce, “Ni ban san wata maraba a tsakanin Baba Hassan da Baba Hussaini ba. Kowanensu na kula da mu ba tare da wariya ko bambanci ba.
“Nakan ji ni kamar a gida nake duk lokacin da nake wajen kowane. Mu ma ’ya’yansu mun hada komai muna gudanar da komai tare kamar yadda muka taso muka gansu.
“Zuriyarmu na zaune lafiya kuma muna farin ciki da alfahari da yadda muka tsinci kanmu. Ba za ka ga wata alamar bambamci ko wariya a tsakaninmu ba,” in ji Ibrahim, babban dan Farfesa Hassan.
An haifi Hassan da Hussaini ne ranar 9 ga watan Agustan 1973 a Unguwar Kawo da ke garin Kaduna.
Sun yi makarantar firamare ta Kaduna Capital da kuma karatun Kur’ani kafin dukkansu su wuce Kwalejin Gwamnati da ke Kano.
Sunan iyayensu Alhaji Isha’k Ibrahim da Maryam Idris. A halin yanzu Hassan da Husain na rayuwarsu a cikin kwanciyar hankali tare da iyalinsu a garin Katsina.
A abinci suna matukar son cin shinkafa da wake, suna sha’awar kallon kwallon kafa musamman gasar Firimiya ta Ingila da ta Zakarun Turai, sannan suna son kallo da sauraron labarai da tafiye-tafiye da bincike a kafar X (Twitter).