✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe

Kungiyar Jama’atu Izalati Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Kasa, ta bayyana cewa ta tura malamai sama da 500 zuwa sassan Najeriya da kasashen duniya…

Kungiyar Jama’atu Izalati Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta Kasa, ta bayyana cewa ta tura malamai sama da 500 zuwa sassan Najeriya da kasashen duniya don gudanar da Tafsirin Al-Kura’ani Mai Girma na watan Azumin Ramadan mai kamawa.

Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce nahiyoyin da Kungiyar ta tura malamai masu Tafsiri kasashen Afirka, Asiya da kuma Amurka.

Ya bayyana haka a wajen bude taron kara wa juna sani na kasa, karo na 28 da Kungiyar ta shirya a garin Jos.

Ya ce, “idan za a tafi wannan aiki na Tafsiri, akwai bukatar a hadu a karantar da juna sanin makamar wannan aiki na Tafsiri, don haka Kungiyar ta shirya wannan taro, na kara wa juna sani.”

Ya yi kira ga malaman da su mayar da hankali wajen sauraron malaman da za su karantar da su a taron da aka shirya, sannan idan sun tafi, su karantar da munate don Allah, da nufin amfanar da al’ummar duniya baki daya.

A nasa jawabin a wajen taro, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman ya yi godiya kan kokarin JIBWIS wajen wayar da kan al’ummar Najeriya.

Ya yi kira ga al’ummar kasar da su taimaka su hada hanu da gwamnati wajen warware matsalar tsaro a kasar.

A cewarsa, “Yanayin tsaro ya tabarbare a kasar nan, don haka dole ne a hada hanu da gwamnati, da sauran al’ummar kasa wajen ganin an magance wannan matsala, domin abin ya fi karfin gwamnati ita kadai.”