✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin ta’addanci: An tube rawanin Makaman Katsina

Tube rawanin wani basarake kan zargin hadin baki da ta'addanci ba sabon abu ba ne a Arewa.

Masarautar Katsina ta tabbatar da tube rawanin Makaman Katsina kuma Hakimin Bakori, Idris Sule Idris bisa zarginsa da tallafa wa ayyukan ta’addanci a gundumarsa.

Kunshin korar Makaman na dauke ne cikin wata takardar wasika da aka rubuta mai dauke da kwanan watan ranar 19 ga Janairun 2023.

Wasikar mai dauke da sa hannun Kauran Katsina wanda shi ne Hakimin Rimi, Aminu Nuhu, ta bayyana warware rawanin Makaman bayan wani kwamiti da gwamnati ta kafa ya same shi da aikata laifukan da mutanensa ke zarginsa da aikatawa.

Kazalika, mai magana da yawun Masarautar Katsina, Ibrahim Bindawa, ya tabbatar da matakin tube rawanin basaraken.

Wannan lamari dai ba shi ne farau na sauke wani basarake a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kan zargin goyo wa ’yan ta’adda baya.

Ko a shekarar 2021, Masarautar Katsina ta tube rawanin Sarkin Pawan Katsina kuma Hakimin Kankara, Yusuf Lawal wanda aka samu da makamancin wannan laifi.

’Yan ta’adda da ke kaddamar da hare-hare ba-ji-ba-gani sun kashe mutane da dama a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya musamman a Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kaduna tare da raba miliyoyi da muhallansu.