✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta yi karar tsohon mijinta saboda rashin ciyarwa da biyan kudin haya

Wata Mata ta yi karar tsohon mijinta a kotun Shari’ar Musulunci dake Magajin Gari a Kaduna akan cewa baya ciyar da ita da ‘ya’yansu biyar…

Wata Mata ta yi karar tsohon mijinta a kotun Shari’ar Musulunci dake Magajin Gari a Kaduna akan cewa baya ciyar da ita da ‘ya’yansu biyar tunda ya saketa. A cewarta, bayan ya daina ciyar da su ya kuma ki biyan kudin haya na dakin da suke zaune ita da ‘ya’yan nasu.

Matar mai suna Maryam Adamu ta shaidawa kotun cewa tsohon mijin nata ya sake ta ne saki daya tun a watan azumin da ya gabata. “Ya sake ni tun a watan Azumi kuma ina da ciki a lokacin amma duk da haka sai ya daina ciyar da ni da kuma ‘ya’yanmu biyar.

“Sannan kuma dakin da muke cikin kudin haya ya kare amma bai biya ba kuma masu daki na zuwa tambaya. Shi yasa na kawo shi kotu domin a taimaka mana ya rika ciyar da mu sannan ya biya mana kudin haya,” inji ta.

Sai dai kuma mijin mai suna Nuhu Abubakar ya karyata zancen matar inda ya ce ba gaskiya ba ne cewa baya ciyar da su. A cewarsa, ita ce ta bukaci da ya sake ta, shi kuma sai ya bi umurninta.

“Ba gaskiya ba ne zancenta cewa bana ciyar da su da kuma cewa wai ban biya kudin hayar dakin da suke ciki ba, na yi maganaý da mai dakin cewa zan biya shi idan na samu kudi,” inji shi.

Alkali Musa Goma ya tunasar da mijin cewa duk da ya saki matarsa a watan azumi kuma a lokacin tana da ciki hakkinsa ne ya rika ciyar da ita da ‘ya’yansu biyar. Dan haka sai ya bukace shi da cewa daga yanzu hakkinsa ne kula da ‘ya’yansa tare da biya masu kudin makaranta da kudin hayar dakin da suke ciki a zaune.