A kwanan baya ne likitoci a kasar Taiwan suka ba da rahoton wata budurwa da aka samu da wasu tsinkaye biyu a cikin fuskarta a tsawon mako guda ba tare da ta sani ba.
Matar mai shekara 29 da aka sakaya sunanta ba ta bayar da rahoton cewa ta je sashin kulawar gaggawa na asibiti ba, bayan fada ya auku a tsakaninta da ’yar uwarta, hakan ya sa ta samu kananan raunuka a hanci da kasan idonta na hagu.
Likitoci sun yi mata hoton X-ray, kuma sakamakon hoton bai nuna komai daga wajen fatar ba.
Matar ta bar asibitin, amma bayan kwanaki sai ta fara jin akwai alamomin ciwo a cikin fatarta wadanda suka fi na farko.
Bayanai sun ce abokiyar fadanta ta yi amfani da wasu tsinkayen roba wajen kai mata hari, inda daga nan ta fara tunanin cewa akwai wasu karyayyun tsinkayen da suka makale a cikin hancinta.
Mako guda bayan yi mata hoton X-ray na farko, ’yar Taiwan din ta koma asibiti, kuma ta fada wa likitoci sababbin abubuwan da ta gano a jikinta.
Wani cikakken bincike da aka gudanar ya nuna guntayen tsinkayen da suka ratsa sassan hancinta suka raba sassan hancin biyu.
Kuma an sake yi mata hoton CT scan wanda ya nuna cewa, akwai guntayen tsinkaye guda biyu da ake cin abincin da su.
Daya tsinken ya kai tsawon inci 1.4 (santimita 3.5) dayan kuwa ya kai tsawon inci 2 (sentimita 5).
Bayan an yi nazarin hoton an gano shigar bakon abu cikin fuskar matar, inda likitoci suka tabbatar da cewa wadancan kananan tsinkayen su ne suka shige cikin fuskarta.
Wani abin mamaki shi ne, ta inda tsinkayen suka shiga cikin kokon kan matar ta nan ne likitoci suka yitiyatar fitar da su, wadanda suke tsakanin kusurwar idonta da karan hancinta.
Matar da aka sakaya sunanta ta bukaci a yi mata tiyatar ce domin cire guntayen tsinkayen, kuma ba ta samu wata matsala ba a yayin tiyatar.
An wallafa wannan rahoto ne a Mujallar Bayar da Agajin Lafiya na Gaggawa ta ‘The Journal of Emergency Medicine’ a ranar 24 ga Yuni, 2021.
Haka kuma, marubuta rahoton sun nanata bukatar a rika gudanar da cikakken bincike, a harkar kiwon lafiya saboda kananan raunuka suna iya boye manyan matsaloli.