Wata mata ta kona marainiyar da take riko mai suna Aisha Muhammad mai kimanin shekaru bakwai a duniya da dutsen guga.
Matar mai suna Hadiza Muhammad wacce take zaune a unguwar Panshekara ta Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ta kona marainiyar ne saboda ta yi kashi a wando.
Wata kungiya mai yaki da cin zarafin jama’a mai suna Association for Social Vices Prevention ce ta yi ruwa da tsaki don ganin an kwato wa marainiyar hakkinta.
Jagorar kungiyar, Malama Rakiya Ladan ta ce ta gano yanayin da yarinyar ke ciki ne bayan da ta kai ziyara asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Ta ce, “Na kai ziyara ne asibitin Murtala don na duba wani mai suna Namama da aka ceto daga daurin shekara bakwai da aka yi masa, kwatsam sai wani jami’in tsaro a wajen yake shaida min akwai wata ma da aka kawo a kan makamanciyar irin wannan azabtarwar.
“Nan da nan na garzaya inda na gane wa idanuna irin mawuyacin halin da take ciki”, inji Rakiya.
To sai dai ta ce ko da suka binciki gidan wacce ake zargin, sai suka gano tuni ta riga ta tsere.
Da take tsokaci a kan lamarin, Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta ce gwamnati za ta yi iyakar kokarinta don ganin ta kwato wa yarinyar hakkinta tare da ganin masu rikon nata sun fuskanci fushin kuliya.
Ta kuma yi alkawarin cewa gwamnatin za ta dauki nauyin kula da ita iya tsawon rayuwarta.