Surukin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Inuwa Uba, ya kalubalanci hurumin kotun da matarsa, Hajiya Balaraba Ganduje, ta maka shi, tana so a datse igiyar aurensu.
Bukatar hakan ta taso ne a yayin zaman Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hokey da ke Kano, ranar Alhamis.
- Mun damka tubabbun ’yan Boko Haram 613 ga jihohinsu na asali – Sojoji
- Za a binciki yadda hannun jariri ya rube a asibitin AKTH da ke Kano
Tun farko dai Balaraba Ganduje ce ta maka mijin nata a gaban kotun tana neman a raba auren nasu, duk da cewa sun shafe shekara 16 tare, kuma suna da ’ya’ya hudu.
Balaraba, ta bakin lauyanta Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa, ta shaida wa kotun cewa ta yi wannan nema ne gaban kotun a karkarshin sashen Shari’ar Musulunci wato ‘Khul’i’ wanda ya ba mata damar fansar kansu daga mazajensu.
Shekarar auren 16, kuma suna da ‘ya’ya hudu
Barista Aliyu ya bayyana cewa sun shaida wa kotun cewa duk da cewar ba su bayyana wa kotun dalilansu na son rabuwar auren ba, amma sun ce a shirye suke su biya wanda suke kara sadakinsa na Naira dubu 50.
Sai dai a zaman da ya gudana ranar Alhamis, lauyoyin wanda ake kara karkarshin jagorancin Barista Umar I. Umar, sun kalubalanci cewa kotun ma ba ta da hurumin sauraren shari’ar.
Hakan ya sa lauyoyin masu kara suka nemi kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci don su mayar wa wadanda ake kara martani.
Alkalin kotun Mai shari’a Khadi Abdullahi Halliru ya sanya ranar 12 ga Janairu, 2023 don sauraren martanin masu kara.
Sai dai lauyan wadanda ake karar ya ce har gobe wanda yake karewa na neman bikon matar tasa, domin su koma su ci gaba da zaman aure, amma ita ta ki amincewa.