✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Super Eagles ta yi sabon koci

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta tabbatar da daukar sabon koci ga babbar kungiyar kwallon kafa…

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta tabbatar da daukar sabon koci ga babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagle mai suna Gernot Rohr.
Kocin, Bature, dan kimanin shekara 63, ya fito ne daga kasar Jamus, Kwamitin zakulo sabon koci ga Super Eagles ne ya bayar da shawarar a dauke shi bayan ya yi wani zama a makoin jiya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin sada zumuntarta na Twitter ta ce “Muna sanar da ku cewa Mista Gernot Rohr shi ne sabon kocin kungiyar Super Eagles kuma tuni ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu”.
Sabon kocin dai ya maye gurbin da Sunday Oliseh ya bari ne tun bayan ya ajiye mukaminsa a watan Fabrairun wannan shekara.
A watan gobe ne ake sa ran sabon kocin zai fara aikinsa a wasan neman gurbin hayewa gasar cin kofin Afirka da Najeriya za ta yi da Tanzaniya kafin daga nan kuma ya cigaba da aikin horar da ’yan wasan a gasar nnman hayewa gasar cin kofin duniya da za a fara a watan Oktoba.
Tuni Hukumar NFF ta tabbatar wa Salisu Yusuf, tsohon kocin riko na kungiyar Super Eagles a matsayin Mataimakin sabon kocin da aka dauka.