✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Suna da mutunci ake samu a aikin jarida ba kudi ba – Umar Tudun Wada

Alhaji Umar Sa’idu Tudun tsohon ma’aikacin gidan Talabijin na NTA Kano ne ya kuma yi aiki da gidajen Rediyon Muryar Jama’ar Jamus da Muryar Amurka…

Alhaji Umar Sa’idu Tudun tsohon ma’aikacin gidan Talabijin na NTA Kano ne ya kuma yi aiki da gidajen Rediyon Muryar Jama’ar Jamus da Muryar Amurka ya kuma taba zama mai taimakawa Gwamna Kwankwaso kan harkokin yada labarai kuma mawallafi babban edita na jaridar sa mai suna Factual, yanzu haka kuma shine Babban Manajan gidan rediyon nan mai zaman kansa na Freedom rediyo FM dake Kano. A hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara aikin jarida da kuma sha’awarsa ga aiki

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

Umar Tudun Wada: Sunana Umar Sa’idu Tudun Wada, an haife ni ne a garin Tudun Wadan dankade a nan Jihar Kano a 1960, a can na yi makarantar firamare daga nan na ta fi Kwalejin Gwamnati ta Kano, wacce yanzu ta zama Kwalejin Rumfa, na samu takardar shaida. Bayan na gama sai na kama aikin koyarwa a firamaren ta Central da ke Wudil na shekara daya, na bari na dawo Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano, aka ba ni mukamin akawu, nan ma ban dade ba na bari na tafi gidan talabijin na NTb Kano kafin ta zama NTA a 1981, a nan ne zan iya ce maka har na fitar da fika a aiki saboda na dade a nan kuma tun ina firamare Allah Ya sa min sha’awar aikin rediyo domin a lokacin akwai rediyon mahaifiyarmu irin katon nan da nake saurara ina jin muryoyin su Lawal Yusuf Saulawa da Lawal Sallau Jibiya da Ibrahim Umaru, kuma Ibrahim Umaru ne ya sa na kara sha’awar aikin rediyo saboda muryarsa. Na fara aiki da NTA ne tun ina dalibi na kai takardar neman aikina a 1979 amma ba a neme ni ba sai a 1981, aka ba ni wannan
Ina aikin jaridar ne har na samu dama na tafi Jami’ar Bayero nan Kano na yi Diploma a bangaren aikin jarida, bayan na gama na sake komawa na yi babbar Diploma a bangaren sha’anin mulki, na sake komawa na samu takardar share fagen digiri na biyu a kan al’amuran da suka shafi ci gaba, ina nan tare da NTA sai aka bude gidan talabijin na jiha CTb sai na bar NTA na koma CTb bayan na share shekara 18 ina aiki da NTA din saboda babu kalubale a aikin tunda na yi ta samun ci gaba domin na fara ne tun daga mai dauko labarai na zama edita na zama babban edita sai ya zama kawai kullum aiki daya nake yi. Yara su dauko labarai in gyara Ingilishin in bayar a karanta, hakan ya sa na ga ba wani kalubale a aikin shi ya sa na ajiye. Ina ajiyewa sai na samu aiki da gidan rediyon Muryar Jama’ar Jamus a matsayin wakilinsu a Kano, ina wa gidan rediyon Jamus din wakilci ne sai Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a zagayensa na farko ya dauko ni ya ba ni mataimaki na musamman a kan harkokin watsa labarai, bayan wa’adinsa ya kare ne sai na sake dawowa aikin jarida inda na kafa wata jarida ta mai suna Factual wacce take fitowa mako-mako ta kuma karbu sosai a wajen jama’a amma da yake harka ce ta kudi sai ba ta jima ba, saboda rashin isassun kudi na gudanar da ita. Ina nan a shekara ta 2003 sai aka bude gidan rediyon Freedom na zo muka fara aiki da su bayan na shekara uku sai Muryar Amurka suka dauki arona na je na yi musu aiki na shekara uku da rabi a can Washington DC. Kuma sai na ajiye aikin na dawo Najeriya yanzu ina nan a Rediyon Freedom kuma ni ne Babban Manaja.
Aminiya: Kasancewar aikin jarida ne kafi dadewa kana yi kuma ka yi shi a Najeriya da Amurka yaya za ka
bambance matsalar aikin a nan da can?
Umar Tudun Wada: Babbar matsalar aikin jarida a Najeriya kama daga kafafen watsa labarai na gwamnati da masu zaman kansu ita ce tsoma baki. Kafar labarai ko ba ta gwamnati ba ce, ba ta tsira daga tsoma bakin hukumomi ba, kai kanka shaida ne na irin gwagwarmayar da aka sha a ’yan watannin baya na wasu gidajen jaridu irin su jaridar Daily Trust da Leadership da wasu jaridu da aka rika bin su a hanya ana kwace jaridunsu, saboda rashin jin dadin wasu labarai da aka buga da suka shafi hukumomin. Ga wanda bai taba fuskantar irin haka ba zai ga kamar tsoma baki ne kawai amma ba tsoma baki ba ne kadai kamar ni da na fara yin jarida na san wahalhalunta zan iya cewa wata dabara ce ta ganin an karya tattalin arzikin wannan gidan jarida saboda idan ka buga jaridarka ta fito sai aka kwace ka ga ’yan kudin da ake sawa a saya a kasuwa za ka rasa su, masu ba ka talla za su daina saboda za su ce kullum ka buga jaridar kwace ta ake yi, ka ga ke nan babu wanda zai iya sayen jaridar balle ya ga tallen da aka yi. Ke nan tsoma baki yana cikin babbar matsalar kafafen watsa labarai a Najeriya. Abu na biyu shi ne rashin ingattatun kayan aiki ga ma’aikata da rashin albashi wanda sai dai kawai sha’awar aikin tasa ka zauna ka ci gaba, kamar kafafen watsa labarai na kasashen waje suna da cikakken ’yancin da ba wanda
yake tsoma musu baki kan yadda suke gudanar da aikinsu. Misali gidan rediyon Muryar Amurka na gwamnati ne amma har na shekara uku da rabi na dawo ban ga inda aka taba tsoma musu baki ba bayan shekara uku da rabi da na yi da na tashi na mika takarduna na barin aiki shugabanin gidan rediyon kirana suka yi suka tambaye ni cewa me ya sa zan bar aikin, albashin ne ya yi kadan ko wani ne ya bata min rai? Idan albashin ne ya yi kadan in fada a kara min. Haka kuma idan ka yi abu na bajinta ba za a gaya maka ba sai shekara ta kare sai ka ga an rubuto maka takardar shaidar yabo mai kyau ana yaba maka har da ’yan kudi za a kara maka. Ka ga a Najeriya kyashi da bakin ciki ba zai sai a yi maka irin wannan karramawar ba. Kuma zai yi wuya ka shekara a kafafen watsa labarai na kasashen waje ba a tura ka kwas ba, yanzu idan muka tattara kafafen watsa labarai na Najeriya guda nawa ne suke bai wa ma’aikatansu takardar inshora? Amma a kasashen wajen ana daukarka aiki da takardar inshora za a hada maka.
Aminiya: Wato kana ganin rashin biyan albashi da hakkokin ’yan jarida da wasu gidan jaridu ke yi na kara haifar da cin hanci?
Umar Tudun Wada: kwarai kuwa ai dama na fada maka domin akwai kafafen labarai anan Najeriya da idan suka dauke ka aiki za su gaya maka ba albashi katin shaida kawai za su ba ka su ce maka ka nema wa kanka mafita su dai bukatarsu kawai ka aika musu da labarai.
Aminiya: Kasancewar ka share shekara 33 kana aikin jarida wane kira ko shawara za ka bai wa ’yan jarida a yanzu?
Umar Tudun Wada: Zan yi kira ga ’yan jarida su tsaya su yi aikinsu yadda ya kamata, kada su dauka aikin jarida aiki ne da zai sa ka yi kudi. A’a sai dai zai sa ka san mutane ka yi suna, kuma idan ka rike aikin da kyau ko bayan ka gama za ka yi mutunci a wajen jama’a. Ba za ka shiga halin takaici ba, abin da ya sa na ce ba aiki ne na yin kudi ba sai suna, idan ka duba kashi 80 cikin 100 na ’yan jaridar da suka bar aiki za ka ga ba masu kudi ba ne, sai dai sun yi suna. Amma idan kudi mutum yake so ya yi to ya shiga aikin banki ko kamfanin man fetur ko ya kama kasuwanci.