✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun zargi mai da’awa da yawan bara

Jama’a sun zargi wani masanin littafin Baibul ya shahara wajen ayyukan da’awa don kira zuwa ga addinin Musulunci mai suna Malam Umar Faruk Okafor, da…

Jama’a sun zargi wani masanin littafin Baibul ya shahara wajen ayyukan da’awa don kira zuwa ga addinin Musulunci mai suna Malam Umar Faruk Okafor, da fakewa da da’awar wajen neman kudi don biyan bukatunsa na kashin kai. Malam Umar Okafor a baya ya rike wani babban coci a Sabon Garin Kano kafin  ya karbi addinin Musulunci kamar yadda ya bayyana wa jama’a a yayin wata lakca da ya gabatar a ranar Asabar da ta gabata a Abuja.

Ya ce ’ya’yansa 8 da suka hada da babbarsu da matarsa, na cikin barazanar rasa imaninsu sakamakon komawa hannun wata ’yar uwar matarsa, wadda ya ce uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ce. Kan haka ne ya ce yana bukatar a taimaka masa da kudin da zai karasa aikin rufe wani gida da ya fara ginawa, don dawo da iyalansa a karkashin kulawarsa.

Wakilinmu wanda yake wajen laccar, ya tattauna da malamin kuma a ranar Litinin da ta gabata ya ziyarci wajen da malamin ya ce yana aikin ginin a unguwar Zamfarawa a garin Masaka da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa. Malamin ya ce shi ya fara aikin ginin wanda ke da dakuna uku kuma yana bukatar abin da zai karasa aikin don kwato iyalansa daga hannun surukarsa wadda ya ce ’yar kabilar Bashama ce.

Sai dai wadansu da suka zanta da wakilinmu a fadar Sarkin Hausawan Masaka, Alhaji Yusuf Umar, sun bayyana malamin a matsayin wanda ya mai da neman taimako a matsayin sana’a, inda suka yi zargin cewa a baya ya nemi taimako da sunan kula da wadanda suka musulunta ko kuma gudanar da aikin Da’awa.

Wani mai suna Malam Kabir Muhammad ya ce kamar shekara shida da suka gabata, malamin ya yi korafin an kore shi daga wani gidan haya saboda haka yana neman taimakon matsuguni na mako biyu.

Ya ce “Na ba shi daki a cikin gidana a kan wannan ka’ida, amma a karshe sai da ya shafe wata shida a gidan, sannan bayan na bukaci ya fita, sai ya tsallaka ya bar iyalansa, “Bai sake dawowa ba sai bayan wata biyu, inda nauyin abincinsu ya koma kaina, bayan ya dawo ne na fitar da kayansa kuma a nan ne na samu ya fita.

Mai Unguwar Zamfarawa inda malamin ya ce ya fara aikin ginin, Malam Ibrahim Usman ya ce lallai ya san Malam Umar Faruk Okafor yana haya a wani gida a unguwar tun da jimawa, kuma ya ce yana da masaniyar cewa ya fara aikin gina gida a kusa da wajen. Ya ce “Akwai malamai da dama wadanda aka haife su a cikin Musulunci ma da suke da hali irin wannan, balle shi. “Ina ganin idan har za a taimaka masa a taimaka masa kawai saboda wannan hali da ya ce iyalansa na ciki,” inji shi.

Aminiya ta tuntubi Hukumar Gudanar da Babban Masallacin Kasa da ke Abuja kan halin da Malam Faruk Okafor ya samu kansa a ciki, inda mai taimaka wa Murshid Farfesa Shehu Ahmad Galadanci, Ustaz Ibrahim Habib ya ce Malam Faruk Okafor yana iya gabatar da korafinsa ga masallacin a rubuce don tantance lamarin tare da nazari a kan yadda za a tallafa masa a kai. Sai dai ya ce ba ya da masaniya ko an gabatar da matsalar a baya kan haka, kamar yadda malamin ya yi zargi a yayin zantawa da wakilinmu.