Sumayyah Shu’aibu Salisu budurwa ce ’yar kimanin shekaru 18 da ta rubuce Al-Qur’ani mai girma da hannunta ba tare taimakon kowa ba a cikin watanni uku.
Yanzu haka dalibar da ke aji biyu a Babbar Sakandire ta kuduri aniyar sake rubuta Littafin Mai Tsarki a karo na biyu.
- Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.98 cikin 100 —NBS
- Rikicin APC: Tsagin Shekarau zai daukaka kara bayan hukuncin Kotu
Wannan budurwa ’yar asalin garin Zariya, an haife ta ne a garin Jega na Kihar Kebbi, amma ta fara karatu a birnin Madina da ke Saudiyya, sa’ilin da mahaifinta, Sheikh Shu’aibu Salisu yake zaman koyon karatu a Jami’atul Madina.
Da take zantawa da Aminiya a garin Zariya, Sumayyah ta ce “bayan da na haddace Al-Qur’ani na kasance mai cike da burin ganin na kuma rubuta shi da hannu na, don haka na sa lokaci kuma na fara.
“Na kwashe tsawon watanni uku ina rubutawa, kuma hakan na da nasaba ne da karancin lokaci da na ke dashi, kasancewar har yanzu ni daliba ce yar aji biyu a Babbar Sakandire ga kuma koyarwa ina yi a Al-Mu’assasa Al-Islah Foundation, makarantar da mahaifina ya assasa a Unguwar Dan Dutse da ke yankin Sabon Layi a Tudun Wadar Zaria.
“Wannan yana cikin dalilan da suka sa na dauki tsawon lokaci ina rubutun, amma ina fata wannan da zan sake rubutawa karo na biyu ba zai kai tsawon lokacin da na dauka a baya ba.”
Aminiya ta ruwaito cewa Sumayyah ta kasance Alarammiya ga Mahaifinta a lokacin gabatar da tafsir na watan Ramadan musamman a lokaci da aka sa dokar hana fita sakamakon bular annobar Coronavirus a 2020, inda take ja masa baki yana fassarawa.
Yanzu haka dai Sumayyah ta ce tana da sauran buri a rayuwarta, “Ina so in zama kwararriya a kan ilmin Komfuta, sannan in kasance shahararriyar malamar addinin musulunci mai sanar da mutane kalmar Allah,” a cewarta.