Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, kan yadda jami’an ’yan sanda ke karbar na goro a kan tituna, da wurin masu laifi ko wadanda ake tuhuma laifuffuka. Kuma matsalar tsaro da muke fama da, ita a kasar nan, musanman Arewacin Najeriya. Matukar hukumar tsaro da gaske take yi, dole ne jami’an tsaro, su daina cin hanci, su yi aiki tukuru tsakanin su da Allah, kuma su rika zuwa wurin aiki da wuri, dole sai lokacin tashi ya yi su tashi. Kuma su rika bincike don kare hakkin ‘yan kasa ga baki daya, ta yadda wani ba zai zo ya bayar da Naira 20 ko 50 ba, sannan ya wuce da kayan laifi. Idan masu tabbatar da doka suka kiyayeta, dole kowane dan kasa ya bi ta sau da ka, wanda kuwa ya ki, to zai fuskanci hukunci, bisa tanadin dokokin kasa.
Daga Abdulsalam Muhammed Tsagem Jihar Katsina 08038792668.
Sakonnin waya
Ga Atiku Abubakar
Tunatarwa ga Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ka tuna irin bambancin da aka nuna maka a jam’iyyar PDP, kuma sai ga shi na ji ka dawo cikin PDM, to wannan jam’iyya ‘danjuma ne da danjimmai.’ Ka koma APC, domin ci gaban Arewa. Daga Malam Kabiru Hamdala Gusau 08066272283.
IMAD ka fito takarar Gwamna
Editan Aminiya, kungiyar matasan PDP na bukatar Bashir IMAD ya tsaya takarar gwamnan Zamfara, saboda daukar nauyin dalibai 50 a fadin Jihar, inda ya biya musu kudin NECO da JAMB, yana da shirin samar da aikin yi ga mutum dubu da 500 a kananan hukumomi 14. IMAD kadai zai iya karya barazanar jam’iyyar APC a Zamfara. Daga Idris Salisu Jihar Zamfara. 08094741817.
Bello Sa’eed ya canci Sarkin Hausawa
Alhaji Bello Sa’eed ya dace ya zama Sarkin Hausawan Birnin Tarayyar Najeria Abuja, don sananne a duk fadin Najeria, kuma yana taimaka wa jama’a ba tare da bambancin addini ko kabila ba. kabilu da yawa sun ba shi sarauta;Yarabawa sun ba shi Otoluse na Abuja; Ibo sun ba shi Omokachi na Anambra, kuma shi ne jagoran al’ummar Juwa Abuja. Masarautar Zazzau ta nada shi Sarkin Samarin Zazzau. Daga Dalhatu Manjos Gobir, Shugaban Zabi Sonka Kulob Samaru Zariya:08036570426
Ga Gwamna Lamido
Aminiya ina so ku mika kukana ga Gwamnan Jigawa, don ya biyamu hakkinmu na tsofaffin kansiloli. Daga Saminu Sule Medi 07030122539.
Yabon gwani
Edit aka ba ni dama in yabi gamji dan kwarai bisa alkairin da yake yi wajen kula da asibiti da marasa lafiya da tsaftar muhallin asibitin Malam-Madori tamkar Turai, wato Abdullahi Mani. Daga Khadija Sani Khallah 07030551978.
Ga Gwamnan Nasarawa
Gaisuwa ga Aminiya, yau kirana ga Aminiya kan Tanko Almakura da ya taimaka wa matan jiharsa, don rage musu yawon sakarci. Daga Malam Danchas Obibo Portharcourt 07037771753
A sa ido kan ’yan sanda
Sufeto Janar na ’yan sanda ka sa ido, wasu ’yan sanda sata suke fitowa ba aiki ba. Su kan kama mutum su sa shi a mota, su kwashe kudinsa, su sake shji. Wasu da kaki, wasu babu. Irin wannan ya fi aukuwa a Legas. Daga A.B B. Katsina Faskari.
Ko jami’an tsaro sun fara fashi?
Fashin da aka yi wa mutanen Kurnar Asabe cikin daren Juma’a, 16 ga watan Agustar bana, ana zargin jami’an ’yan sanda. Domin da kayan sarki suka zo, suka bata lokacinsu a gidajen talakawa. Tunda hukuma ta kasa ba mu kariya, wajibi ne mu tsara dabarun tsaro. Allah Ya tona asirin wadanda ke da hannu a jami’an tsaro da sauran batagari. Amin. Daga Manara Shehin Babbar Kuka.
Ga al’ummar Tiga
Salamullahi alaikum. Al’ummar Tiga mu kula da wuraren ibada, don Allah na son tsaftar tsarki da tsarkakewa. Mu daina daure dabbobi jikin Masallacin Juma’a; a daina yin shanya a wurin. Allah Mai kyau ne, Ba ya karba sai mai kyau.’ Daga Ahmad Tiga 08068643445
Mu yi adalci
Rashin gaskiya da adalci ke haifar da rashin zaman lafiya a mafi yawan kasashen mu na duniya. Da za mu daure, mu cire son zuciya da kwadayi, kuma mu kori sauya halayyarmu, mu yi watsi da dabi’u marasa kyau. Babbu shakka da munga sauyi a rayuwa. Japan dasauran kasashen duniya su zame mana mislai. Daga Isa Kwafsi 08087436699.
A dauki mataki kan jami’an tsaro
Shugaban hukumar ’yan sanda, ka sani matukar ba a dauki mataki kan jami’an tsaron da suke yi wa al’umma fashi a gidaje da tituna ba, to za a ga mummunan sakamako. Domin wajibi ne daukar fansa da neman hakki. Allah Ya sa ku gyara. Daga Sharhabilu danmai littafi Kirikasamma.
’Yan Hadeja ku yi hakuri
Al’ummar Hadeja da kewaye ganin yadda ambaliya ta sakomu a gaba, kuma gwamnatinmu ta manta da mu, inda a ce Dutse ake yi, to wallahi da matsalar ambaliya ta zama tarihi. Kar mu damu akwai Allah. Daga Yahaya Ahmed Jabo K/Hausa G. Jigawa 08026392800.
A daina bangar siyasa
Matasa banga ba ta cikin tsarin siyasa. Talakawa ku hana ’ya’yanku bangar siyasa da cin zarafin jama’a da sunan siyasa. Don Allah ku taimaki gwamnati wajen wanzar da zaman lafiya da dora matasan kasar nan kan tafarkin kishin kasa. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.
Jaje ga dan majalisar Malumfashi
Editan Aminiya ka mika jajena ga Abdul dan Bakara, wato Babangida Ibrahim Mahuta, bisa bugu da tozartawar da aka ce jama’ar mazabarsa sun yi masa, don huce haushi. Sai a rika kula don a tsira da mutunci da dukiya. Daga Jamil Medicine Malumfashi. 08039515906.
Jaje ga al’ummar Talatar Mafara
Salam Edita. Bayan wannan ina so ka mika min sako jaje ga al’ummar T/Mafara na Jihar Zamfara dangane da ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan garin. Muna fatan alheri. Hukumomi a taimaka. Daga (KGY) Bindawa 08034934730.