✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sudan: An kashe mutum 138 a sabon rikicin kabilanci a Darfur

Likitoci sun ce yawancin mace-macen sun faru ne saboda rashin isassun kayan aiki a cibiyoyin lafiyar da ke yankin.

Akalla muutm 138 ne aka kashe a wani sabon rikicin bakilanci da ya barke a yankin Darfur na kasar Sudan.

Jami’an lafiya a yankin ne suka bayyana haka ranar Alhamis, suna masu cewa yawancin mace-macen sun faru ne a sakamakon rashin isassun kayan aiki a cibiyoyin lafiyar da ke yankin.

“Yawacin mutanen da suka samu raunkuna sun rasu ne saboda ba a iya ba su kulawar da ta ce ba a cibiyoyin lafiya saboda rashin isassun kayan aiki,” a cewar kungiyar likitoci reshen Arewacin Darfur.

A ranar 17 ga watan Nuwamba ne sabon fada ya kaure tsakanin Larabawa masu kiwon rakuma a yanin Jebel Moon da ke Arewacin Darfur.

Daga baya a ranar Asabar wani fadan ya sake kaurewa a yankin Krink da ke Darfur tsakin wasu bangarori da ba sa jituwa da juna, dauke da manyan bindigogi.

Kungiyar likitocin yankin ta ce mutum 138 aka kashe, cikinsu har da wasu mutum 25 da aka kashe a Jebel Moon a ranar Laraba da wasu 106 da suka samu raunuka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 22,000 ne sabon rikicin ya raba da muhallansu, ciki har da wasu mutum 2,000 da suka tsallaka zuwa kasar Chadi domin zaman gudun hijira.

A shekarar 2003 ne yankin ya fara daidaicewa bayan yakin basasar da ’yan tawaye daga kananan kabilu suka tayar da kayar baya saboda zargin gwamnatin Omar al-Bashir ta lokacin da yi wa kananan kabilun da ba Larabawa ba danniya.

Tayar da kayar bayan tasu ce ta sa Gwamnatin al-Bashir ta yi amfani da wasu ’yan sa-kai da ake kira Janjawid ta murkushe su.

Sai dai kuma ana zargin mayakan Janjawid din da kisan gilla, yi wa mata fyade, yin fashi da kuma kona kauyuka.

Akalla mutum 300,000 ne aka kashe a rikicin na 2003, baya ga wasu miliyan 2.5 da ya raba da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.