An garzaya da tsohon Shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir, asibiti daga gidan yari domin duba lafiyarsa.
Lauyansa ya ce an kai Al-Bashir asibiti ne a ranar Lahadi domin ci gaba da jinyar sa kan cutar koda da hawan jini da yake fama da su a gidan yari.
- Matakin G7 na karya farashin man Rasha ya fara aiki
- An kona ofishin gwamna kan tsadar rayuwa a Syria
Al-Bashir mai shekara 78 na tsare a gidan yari a yayin da ake ci gaba da sauraron shari’arsa kan zargin juyin mulki da ya yi a 1989.
Bayan shekarar 40 yana mulki, aka kifar da gwamnatinsa a 2019 bayan tarzomar da ta tashi kan tsadar burodi a kasar.
A ranar Talata ta makon jiya ne lauyoyi suka roki kotu ta ba da iznin kai shi asibiti, saboda barin sa a gidan yari da hawan jini da cutar koda ba tare da an yi masa magani ba na iya zama barazana ga rayuwarsa.
Idan ba a manta ba, ganin hotunan Al-Bashir yana tattaki a dakin asibiti ya tayar da kura a farkon shekarar nan.