Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma’aikatan Jami’o’i Marasa Koyarwa (NASU), sun dakatar da yajin aikin da suke yi.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata takaitacciyar ganawa da shugabannin kungiyoyin suka yi da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ranar Asabar a Abuja.
- Ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 a Kano da Jigawa
- Dalilin da sojoji fiye da 200 za su ajiye aiki —Nwachukwu
A cewar Ministan Ilimin, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 50 don biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU da NASU da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
Da yake zantawa da Aminiya, Shugaban SSANU, Kwamared Haruna Ibrahim Mohammed, ya ce janyewar yajin aikin takaitacciya ce ta tsawon watanni biyu kacal.
Ya ce sun cimma yarjejeniyar ce da zummar bai wa Gwamnatin Tarayya damar cika alkawuran da ta dauka a tsakanin wannan lokaci.
Haruna ya ce muddin gwamnati ta ki aiwatar da yarjejeniyar a cikin kwanaki 60 masu zuwa, za su koma yajin aikin.
A cewarsa, dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Laraba ta makon gobe.
Sai dai ana sa ran ayyuka za su takaita a jami’o’i la’akari da cewa har yanzu ASUU ba ta sauya matsayarta ba.
Ana iya tuna cewa, kungiyoyi sun tsunduma yajin aiki ne a tun a watan Maris, makonni kadan bayan kungiyar ASUU ta shiga nata yajin aikin kan abin da suka kira gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.
A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda, sai dai daga baya kungiyar ta mayar da yajin aikin na sai abin da hali yayi.