✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sonsomin raba Najeriya: Wa ya ki a dama, kuturu ko mai maho?

Daga lokaci zuwa lokaci, wasu yankuna ko kuma a ce wasu rukunnan mutane kan motso da yunkurin raba kasar nan, kowa ya kama gabansa. Suna…

Daga lokaci zuwa lokaci, wasu yankuna ko kuma a ce wasu rukunnan mutane kan motso da yunkurin raba kasar nan, kowa ya kama gabansa. Suna ganin wai yankinsu yana da dukiyar fetur. Suna ganin cewa al’ummar Arewa, wadanda suka dade suna kira da sunan ’yan-cima-zaune, za su sha wahala idan aka raba. Ni kuwa na ce, anya dai? Shin wai a wannan batu na neman raba Najeriya, wa ya ki a dama, kuturu ko mai maho?
Ko ka taba zama ka tambayi kanka game da wadannan al’amura da suke gudana? Ina magana ne game da al’amuran da suka shafi zamantakewa tsakanin kabilu da da sassan kasar nan. Ka taba tambayar kanka cewa, shin a da can kafin a ce an hada sassa da yankunan kasar nan, aka kirkiri Najeriya, shin  yaya al’ummun kasar nan suke zaune? Haka kuma, bayan da Turawan Yamma suka yi abin da suka yi, suka cakude mu zuwa dunkulalliyar kasa mai suna Najeriya, yaya aka zauna tun daga farko, har zuwa lokacin da yankin Inyamurai ya fara hankoron yancin neman kasar Biyafara? A yanzu kuma da ake ta wannan hauma-hauma, yaya muke zaune? Idan an raba kasar, me zai faru kuma wane yanki ne zai balbalce, ya rasa tudun dafawa? Amsoshin wadannan tambayoyi ne ya kamata mu yi, madamar muna son rufe bakin tsanya, wato idan muna son a daina yi mana barazana da batun raba kasa.
Tun farko ma abin da ya kamata a tambayi masu son a raba Najeriya shi ne, shin gida nawa za a raba ta? Raba ta za a yi ta fuskar kabila ko yanki? Shin za a raba ta biyu ne tsakanin Arewa da Kudu ko kuwa? Idan haka ne, yaya zama zai kasance tsakanin al’ummun Yarabawa da Inyamurai da kuma sauran kananan yaruka na yankin Neja-Delta?
Mu dauki misalin ma a ce to mun amince a raba kasar zuwa biyu, Arewa da Kudu, to idan an raba din, yaya abin zai kasance? Ni kuwa na ce madamar muka natsu muka yi nazarin yanayi da tarihi, muka kalli abin da zai je ya zo, babu shakka babu abin da zai tsoratar da Arewa idan ta samu cin gashin kanta, a matsayin kasa.
Idan muka dauki batun mulki da siyasa, yankin Arewa sai dai ya koya wa wani yanki yadda ake yi. Su kansu Turawan mulkin mallaka, sun samu yankin da tsarin gudanar da mulki mai inganci da wayewa. Idan an raba kasar, abu ne mai sauki al’umar Arewa su iya gudanar da tsarin mulki mai inganci da dacewa, yadda za a gina kasa bisa doka da oda. Mulkin da zai wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Idan muka duba batun addini da al’ada kuwa, nan ma sai mu ce son barka, domin kuwa al’adunmu kyawawa ne masu dauke da basira da wayewa. Ta fuskar addini kuwa, idan muka duba kuma muka yi nazari, ko a can baya kuma ko a yanzu, kowane irin addini da ake a Arewa, da gaske ake yinsa. Idan ka duba yanayin mabiya addinin Kirista da ke Arewa, za ka same su sun fi tafiyar da addinin bisa gaskiya daidai gwargwado fiye da kininsu na Kudancin kasar nan. Haka ma batun yake idan ka duba mabiya addinin Musulunci, na Arewa sun fi inganci fiye da na al’ummun Kudanci. Don haka za a iya amfani da koyarwar addinanan, a samu hadin kai da juna, a samu zaman lafiyar da za ta samar da ci gaban kasa.
Wani al’amari da ake kallo ana yi wa Arewa gori, har ake son a raba kasar saboda shi, shi ne arzikin fetur. Ana ganin cewa fetur din ne babbar kafar kawo wa kasar kudin shiga, don haka da zarar an raba Najeriya, za su mallake shi su kadai, kuma ga su ’yan tsiraru. Ni kuwa na ce bayan tiya akwai wata caca, domin kuwa ba nan gizo ke sakar ba, wajen fiidda abawa.
Ga masu wannan hasashen, su saurari wannan batun: Allah Ya albarkaci Arewa da ingantattar kasar noma, inda za ka iya noma duk wani tsiro da kake so mai albarka kuma a same shi. Idan ka dauki gyda, za ta iya samar da kudin shiga fiye da fetur. Litar fetur daya ba ta kai Naira dari ba, amma nawa ake sayar da kwalbar mangyada, wadda ba ta kai ma lita daya ba? Ana sayar da ita Naira dari biyu ko ma fin haka. Kuma wahalar da ake wajen tace fetur, ba ita ake yi wajen matse mangyada daga tunkuza ba. Mace na zaune ma a gida za ta iya haka, wanda haka zai kara bunkasa sana’a da tattalin arzikin kasa.
Idan ka dauki auduga, ka dauki ridi, ka dauki dabbobin da Allah Ya hore mana, za ka ga cewa arziki na gani-na-fada yana nan Arewa. A yanzu haka, fata ko kirgi, ita ce ta biyu wajen samar da kudin shiga a Najeriya. Idan ana batun fetur da iskar gas din ma, akwai su kimshe a Arewa. Siyasa ce kawai ta hana a maida hankali wajen hako su. Idan kuwa aka raba kasar, shi ke nan an samu damar cin gajiyar wannan dukiya.
Baya ga wadannan, Allah Ya albarkaci yankin Arewa da sauran ma’adanan kasa masu daraja, kamar gwal da zinare da sauransu. Don haka, idan ma har an ce za a raba kasar nan, to ina ganin Arewa ba ta da damuwa, madamar dai za a maida hankali wajen fuskantar gina kasa da gaske.

Albishirinku Gizagawa!

Ya ku Gizagawan Zumunci, ina yi muku Barka Da Sallah!
Ina yi maku albishir da cewa, an dawo da rijistar Gizagawa. Ana kira ga shugabannin Gizagawan Jihohin kasar nan da su tattara sunayen tsofaffin membobin da ba a jaddada rijistarsu ba, su aiko domin a jaddada masu.
Ga sababbin masu son yin rijista a wannan kungiya mai albarka, sai buga wa Madugun Gizagawa ta wannan lambar: 08098157899, domin karin bayani.
**
A wannan makon ga wanda ya dace da rijista: Malam Nasiru Ya’u, 08065616033 (GZG594ABJ).
Ina sanar da daukacin Gizagawa cewa Malam Nasiru daya ne daga cikin manyan ma’aikatan kamfanin Media Trust Limited da ke wallafa jaridar nan ta Aminiya, don haka muna yi masa barka da shigowa cikin wannan tawaga ta Gizagawan Zumunci.