✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Amurka ba su kai samame ba —Mazauna Abuja

Kakakin ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce ba su samu wani rahoto makamancin wannan ba.

Mazauna Abuja sun musanta batun cewa sojojin Amurka sun kai samame rukunin gidajen Trademore da ke Lugbe a Abuja.

A ganawar wakilinmu da wani mazaunin yankin, ya ce gaskiya ne an kai samamen, amma jami’i daya ne tak dan kasar waje a ciki.

A tataunawarta da Aminiya ranar Laraba, Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce ba su samu wani rahoto makamancin wannan ba.

Shi ma dai wani Mataimakin Sufirtandan ’yan sanda ya musanta batun da ake yadawa cewa Hukumar Tsaro ta DSS da Sojojin Amurka sun gano wasu akwati cike da bama-bamai.

“Ina magana da Kakakin ’Yan Sandan yankin, ya kuma bayyana min cewa ba gaskiya ba ne batun, sai dai ka tuntubi DSS ka ji,” inji Josephine.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar tsaron DSS din Peter Afunanya ranar Laraba, bai amsa kiran wayar da ya yi masa ba, sai washegari Alhamis.

Amsar da ya ba wa Aminiya, ya ce tabbas wannan labarin kanzon kurege ne.

A cikin sanarwar dai da aka yada ta yanar gizo, an gargadi mazauna yankin rukunin gidajen da su kasance masu lura sosai, saboda abinda ka je ka zo.

%d bloggers like this: